1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata na fuskantar koma baya a duniya

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 16, 2020

Asusun kula da yawan jama'a na Majalisar Dinkin Duniya ya kaddamar da rahoto a kan halin da al'ummar duniya ke ciki a wannan shekara ta 2020.

Symbolbild | Welt Bevölkerung
Yadda al'umma ke kara yawaita a duniyaHoto: picture-alliance/Zoonar

Rahoton na wannan shekarar da asusun kula da yawan al'umma na Majalisar Dinkin Duniyar ya kadammar dai, ya mayar da hankali ne a kan koma bayan da mata ke fuskanta a duniya, kama daga yi masu kaciya da fyade da hana su samun karatun boko, abin da asusun ya ce duka ya sabawa hakkokinsu. Taken rahoton na bana dai shi ne: "Ba da izni na bane. Kaucewa duk wasu halayen da ke illa ga mata da 'yan mata a kokarin samun daidaito."

Madam Kori Habib jami'a ce a asusun na Majalisar Dinkin Duniya da ke Najeriya, ta ce koda yake nazari ne a kan al'ummar duniya baki daya, amma sun gano wadanda matsalar tafi shafa. Rahoton yace mata sama da milyan hudu ne ke fuskantar matsalar kaciya a wannan shekarar, To ko wane hali ake ciki a Najeriya a kan  kalubalen da ke fuskantar mata a daidai lokacin da yawan al'ummar ke karuwa a kasar?

Al'ummar Najeriya na yawaitaHoto: AP

Hajiya Saudat Shehu Mahdi ita ce sakatriyar gudanarwa ta kungiyar kare hakkokin mata da yi musu adalci wato RAPA, ta kuma nunar da cewa cikin matsaloli 19 da ke da nasaba da al'ada ko kuma tsarin rayuwa da ba na shari'a ba ko dokar kasa, kaciyar mata da auren dole. Hajiya Saudat Mahdi ta kara da cewa kiddigar duniya ta nunar da cewa a Najeriya ne ake da kaso daya bisa hudu na wannan matsalar.  

Tun da farko dai wakiliyar asusun kula da yawan al'ummar na Majalisar Dinkin Duniyar Ulla Mueller ta ce, lokaci  ya yi da za a dau matakan gyara: "Idan akwai abu daya da zai burge ni shi ne a bullo da dabarar da za mu kawo karshen wannan matsala a Najeriya, ina jin lokaci ya yi da za a sauya, ina jin ya kamata su canza tunanin yadda muke tafiyar da al'amauranmu."

Najeriya dai kasa ce da yawan alumarta ke karuwa a kowace shekara tare da hasashen zai iya ninkawa nan da shekara ta 2050, a yanayi da al'umma ke fuskantar hali na rashin wadatuwar abubuwan more rayuwa da ke nuna bukatar cin moriya da albarkar da ke tattara da yawan alumma a kasar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani