Yawan bude ido a Kamaru
March 16, 2012
Kasar Kamaru na daya daga cikin kasashen Afirka da masu yawan bude ido ke bukatar ziyarata, to saidai masu kula da harkar yawan bude ido na kasar, na zargin gwamnati da yin sako-sako da wannan sana'a.
Daga masu yawan bude idan har da 'yan kasar ta Kamaru da kuma da dama da ke zuwa daga sassa daban-daban na duniya.Marie Louise Liti wata 'yar asulin Kamaru ce wadda ke zaune a Faransa ta zo tare da yaranta a wanan wurin kallo:
"Mun zo ne a matsayin 'yan yawan bude ido, ina bukatar nunawa yarana namun daji kala-kala, hasali ma manyan birrai, a cen Faransa ma akwai birran to amma babu irin wanda muka gani a nan."
Dubunan 'yan kasar Kamaru da masu daga ketare na cincirindo ko wace rana wurare dadaban-daban na yawan bude ido ,to amma a cewar Baro Jamen wani masanin wannan harka, har yanzu akwai sauran rina kaba wajen inganta yawan bude ido a Kamaru:
"Shi yawan bude ido sana'a ce tamkar noma,kiwo aikin hannu to amma har yanzu masu sana'ar ba su dauke ta da mahimmancin da ya dace da ita, kame-kame ne kadai su ke yi".
To amma a tunanin Emmanuel Ngassa Happi shugaban haddadiyar kungiyar masu kamfanonin yawace-yawace na Afrika ta yamma da ta tsakiya bugu da kari shugaban kamfanonin yawan bude ido na kasar Kamaru,gwamnati ce ba da dauki al'amarin da daraja ba, ya kara da cewa:
"Abun dake bamu takaici shine yadda gwamnati kewa harkar yawan bude ido daukar sakainar kashi.Yau shekaru 15 kenan da muke bi bayan gwamnati domin ta shimfida dokoki a hukunce, wanda za su tsara harkar, to amma har yanzu shiru, ta kaka mutum zai sakankance ya zuba dukiyarsa cikin sana'ar da ba ta da tsari."
Duk da rashin tsarin da masu sana'ar yawan bude ido ke korafi da ita, gwamnatin Kamaru ta kiyasta cewar ko wace shekara akwai akalla mutane dubu 500 dake shigowa kasar da sunan yawan bude ido, dubu 300 daga wannan baki na bi ta birnin Douala mai filin saukar jiragen sama irin na zamani da kuma tasahar jiragen ruwa.
To saidai babu cikkakun alkalluma na yawan 'yan Kamaru dake ziyartar wuraren cikin kasar da sunan yawan bude ido.