SiyasaGabon
Yawan Juyin mulkin sojoji a Afirka
August 30, 2023Talla
Sojojin da suka fito ta kafar talabijin, sun bukaci kowa da kwantar da hankali a kasar, suna mai bayyana himmatuwarsu ga girmama manufofin Gabon da ta kasa-da-kasa.
Cikin jawabin da ya gabatar guda daga cikin sojojin ya ce sun soke zaben da hukumar zabe ta sanar da shugaba mai ci Ali Bongo a matsayin wanda ya yi nasara da kundin tsarin mulki da majalisun dokokin kasar da ma sauran hukumomin gudanarwa a Gabon.
Gwamnatin Gabon din dai ta sanar da kafa dokar hana zirga-zirga a fadin kasar baya ga katse hanyoyin sadarwar Intanet da aka yi
Duk wani zabe da aka gudanar a kasar mai arzikin Mai, na karewa ne da rigingimu tun a shekarar ta 1990 da ta koma tsarin jam'iyyu barkatai na siyasa.