1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sami raguwar masu neman mafaka a kasashen Turai

Binta Aliyu Zurmi
January 11, 2025

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana samun raguwar masu neman mafaka da kusan kashi 12 cikin dari a shekarar da ta gabata.

Russland Grenze zu Estland | Migration, Flucht
Hoto: Margus Ansu/Scanpix/IMAGO

A cewar hukumar bayar da mafaka ta kungiyar EU, hukumar ta yi rajistar mutane sama da miliyan daya ne a kasashen kungiyar EU 27 da Norway da kuma Switzerland.

Mafi akasarin wadanda suka saka bukatar neman mafakar a cewar hukumar sun fito ne daga Siriya da ke da kaso 15 cikin dari sai Afganistan da ke da sama da kaso 8 da Venuzuela da ke biye mata sai kuma kasar Turkiyya.

A ranar Alhamis din da ta gabata ofishin da ke kula da kaurar jama'a da 'yan gudun hijira da ke Jamus ya bayyana cewar adadin masu neman mafaka a kasar ya ragu da kusan sama kaso 30.

Ragowar sama da mutum dubu 100 ne aka gani a Jamus din idan aka kwatanta da yawan da aka gani a shekarar 2023.

Jamus dai na zama a sahun gaba na kasashen EU da ta fi samun tururuwar yan gudun hijira. 

 

Karin Bayani: 'Yan gudun hijira sun fara komawa Siriya