1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YAWO YA KAI WANI MAI KOYON SANA'A A NAMIBIYA.

Yahaya Ahmed.January 28, 2004
Michael Frahn, wani saurayi ne mai sha'awar koyoyn sana'ar kafinta tun yana yaro. Sabili da haka ne kuwa, bayan ya gama makarantarsa ta Sakandare, ya shiga cikin kungiyar nan ta masu koyar sana'ar hannu. Bayan ya dan jima yana koyar sana'ar, bisa tsohuwar al'adar da ake bi a nan Jamus ne, lokaci ya zo da ya kamata, ya shiga duniya, yana bi gari gari ko kuma kasa kasa don ya koyi fasahohi daban-daban da ake da su a sana'ar da ya zabar wa kansa. Ta hakan ne dai, ya sami damar zuwa birnin Windhoek na kasar Namibiya, inda zai taimaka wajen yi wa wani ginin Hotel a babban birnin kasar rufi. Ya dai sadu da wasu takwarorinsa biyu kuma daga Jamus a Namibiyan, inda tare suke aiki a gun gina wannan Otel din.

daya daga cikinsu, Lutz Hildebrandt, ya bayyana irin aikin da suke yi:-

"Wannan wani katako ne da za a lankwasa, a hada shi da wasu itatuwa, wadanda a kansu ne za a dora rufin. Za a shirya wasu katakan kuma, wadanda za a yi amfani da su wajen fida da tagogin da za a yi wa ginin."

Ginin dai, ba na siminti ba ne kawai. Gini ne na gargajiya irin wadanda ake da su a nan Jamus. Sabili da haka ne kuwa, masu Otel din suka yi kokarin samo wadannan masu sana'ar hannun don su tayar musu da ginin kamar yadda suke bukata. Hildebrand ya kara bayyana cewa, akwai wasu matsaloli da suke huskanta, wadanda ba a samunsu a Jamus. Amma duk da haka suna kokari dai su ga cewa, ana samun ci gaba.-

"A Jamus, idan ka ce gobe da karfe 8, ya kamata a sami katakan nan a gun aiki. To babu shakka, za ka same su da karfe 8 din. Amma a nan sai mu yi sati 2 muna jiran katako. To ba laifinsu ba ne, daga Afirka Ta Kudu ake samo katakon."

Su dai wadannan masu koyon sana'ar, ba aikin kafintan kawai suke yi a gun ta da wannan ginin a Namibiya ba. Ana tinkararsu da matsaloli daban-daban da ba su shafi aikin kafinta ba. A lal misali Hildebrandt ya bayyana cewa, a wasu lokutan su suke zane na wasu bangarorin ginin, wadanda ba a fid da su sosai a zanen ginin gaba daya ba.

A hankali dai, duk da tafiyar hawainiyar da suke yi, wadda ba su saba da ita a nan Jamus ba, Hildebrand da takwaroinsa sun kyautata zaton cewa, za su kammala ginin kafin karshen watan Fabrairu.

Michael Frahn, shi ma ya bayyana cewa, an dade ana irin wannan ginin na gargajiya a Jamus. Kuma:-

"Kamar yadda muke ta da ginin na dai, mun tabbatar cewa zai tsaya sosai, kamar dai a Jamus. Can akwai gine-gine irin wannan, wadanda tun fiye da shekaru dubu da suka wuce ne aka gina su. Irin wadannan gine-ginen su suka fi dadewa a duniya."

A Namibiyan dai akwai Jamusawa da yawa da suka yi kaka gida a can. Su ne kuwa, idan sun tashi yin wani muhimmin gini, suke tunawa da irin fasahar da kakannin kakanninsu suka yi amfani da ita a da, su kuma yi kwaikwayo da ita. Sabili da hakan ne kuma, suke nemo kwararrun ma'ikata don su gudanad da aikin ginin.

Wadannan masu sana'ar hannun daga Jamus dai sun ce sun gamsu kwarai da zaman da suka yi a Afirka. Kuma, bayan wannan ginin ma, za su tsawaita zamansu a Namibiyan, idan sun sami wata kwangilar kuma.