Yaya ci gaban kasashen Afirka renon Faransa?
August 25, 2025
A cikin wannan shekara kasashe da dama na nahiyar Afirka ke cika shekaru 65 da samun 'yanci daga Turawan mulkin mallaka, ciki har da Najeriya, da Somaliya amma galibin kasashen sun kasance rainon Faransa inda ake da kasashe 14. Wannan lokaci na zuwa lokacin da Shi kansa Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya tabbatar da cewa akwai tsamin dangantaka tsakanin Faransa da wasu kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka a Afirka. Sai dai a cewar Shugaba Alassane Ouattara na kasar Cote d'Ivoire kasashen na Afirka sun taso:
"Shekaru 65 lokaci ne na bunkasa. Lokaci ne na sanin abin da ya dace, mun kawo karfi. Za mu gina gaba daga abin da muka sani."
Wasu kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka suna sahun gaba na fama da talauci tsakanin kasashen Afirka, bisa mizanin ci-gaban dan Adam. Gwamnatoci da mutanen kasashen suna ci gaba da samun kalubale mai tsauri. Ga misali kasashen yankin Sahel irin Mali, da Burkina Faso, da Jamhuriyar Nijar gami da Chadi suna baya ga dangin kan duk wasu alkaluman ci-gaba.
Matthias Basedau daraktan cibiyar kula da harkokin ci-gaban kasashen Afirka da ke birnin Hamburg na Jamus ya ce kasashen suna fama da yanayin kasa da ba ba za a iya nomawa ba, ga karuwar mutane cikin hanzari fiye da yanayin ci-gaban da ake samu sannan ya kara da cewa:
"Akwai kalubale na smaun zaman lafiyar siyasa. Wannan cikin sauki ake samun rikici na tarkon da aka dana, abin da ake gani ke nan. A hankali ana kara samun rikice-rikice. Gwamnatocin farar hula kafin sojoji su yi juyin mulki a wasu kasashen, gwamnatocin ba sa iya mayar da martani na rikice-rikicen bisa hanyar da 'yan kasa za su gamsu."
Bayan shekara da shekaru a karshe dai gabilin kasashen sun sallami sojojin Faransa da suke da sansanoni. Sai dai har yanzu akwai sauran aiki kan ci-gaban siyasa a kasashen. Tumba Alfred Shango Lokoho masanin tarihi da ke Jami'ar Sorbonne Nouvelle na kasar Faransa:
"Mun yi imani daga taron kasa na shekarun 1990 mun shiga sabon tsari na samun cibiyoyin gwamnati da ke da karfi. Mun gani akwai koma-baya da aka fuskanta. Yau galibin kasashe Afirka, suna tare da shugabannin da suke ci gaba da mamaye madafun iko, tare da sauya kundin tsarin mulki domin ci gaba da babakere. Wannan shi ke kassara lamura a nahiyar. Muna bukatar cibiyoyin gwamnati masu karfi."
Duk da cewa tasirin Faransa da sauran kasashen Yamma ya ragu a kasashe rainon Faransa shekaru 65 bayan samun 'yanci, amma har yanzu kasashen na taka rawa wajen samar da kayayyakin da masana'antun kasashen Yamma ke bukata. Kuma tashin farashin kayayyaki a kasashe rainon Faransa bai kai wanda ake gani a kasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka ba.