1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaya hallitar jinsi ta ke sauyawa?

May 27, 2025

Hallitar jinsi na da fadi. Daukar hankali na Jinsi yana faruwa ne a lokacin balaga sakamakon ayyukan kwayoyin hallitar dan Adam da kuma wasu dalilai da suka shafi kwakwalwa da yanayin zamantakewa.

Schweiz LGBT Demonstration Gesetz Referedum Ehe für alle
Hoto: Glories Francois/Abaca/picture alliance

Shekaru 35 da suka gabata wato a tsakiyar watan Mayun 1990 ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta kafa tarihi wajen nesanta dabi'ar neman jinsi guda da matsala ta Rashin lafiyar kwakwalwa.  An dai kwashe gomman shekaru a duniya, ana baiyana kauna tsakanin jinsi guda a matsayin larura, da ta tilasta daukar matakai masu tsauri ciki har da dauri a gidan yari ga wadanda ke neman jinsinsu guda. 

Gabanin shekara ta 1990, dabi'ar nema ko auren jinsi daya, aba ce da aka dauka babbar matsala a fadin duniya, abin kuma da ya jefa miliyoyin wadanda ke samun kansu cikin lamarin cikin matsaloli iri daban-daban.

Sai dai ilimin kimiyya ya jima da nuna cewa wannan dabi'a da haka ake halittar mutane da ita, ba wai kawai tsananin fandarewa ce ko zabi da ke zuwa daga wajen masu ita ba.

Hoto: Privat

Masana sun ce tsari ne na bambancin da ke tsakanin bani Adama ta fuskar dabi'a ko halitta.

Farfesa Klaus M. Beier, babban masanin tsarin halittar dan Adam ne da ke aiki a asibitin Charité da ke birnin Berlin, ya yi karin bayan kan wannan batu na kawai mutum ya tashi ya ji shi da kauna ko soyayyar jinsinsa haka kawai.


"Ai babu mutumin da ya zabi irin halittar da aka yi masa namiji ko mace, ko kuma inda sha'awarsa ta karkata. Sha'awa dai abu ne da ke faro wa mutum a lokacin da yake balaga sakamakon sauyin jiki da sinadaran halitta ke kawo shi. Idan har ta zo wa mutum fa, to hakan za ta zauna har abada. Kokarin kuma sauya shi, iya yin mutum ba abu ne da ke iya yiwuwa ba."


Said ai duk da wannan matsayi na ilimin kimiyya dangane da dabi'ar da mutum kan samun kansa a ciki, har yanzu masu neman jinsi na nan suna fama da tsangwama a wasu yankuna na duniya.

Hoto: Jelena Djukic Pejic/DW

Misali kasashe 67 na duniyar, na daukar wanda ke son jinsinsa wato mace ta so ‘yaruwarta mace ko namiji ya nuna soyayyarsa ga danuwansa namiji, babban laifi ne na doka, inda har ma ta kaiga kasashe bakwai daga ciki, laifi ne na kisa.

Kuma kusan rabin wadannan dokoki masu tsauri, to suna kasashen Afirka ne inda kasashe 22 ne na nahiyar daga cikin 54, suka halasta auren jinsi ko nema tsakaninsu."

Farfesa Klaus M. Beier kwararren masanin jinsi a Berlin, ya ce iya kokarin da mutum za iyi na sauya wannan tsari na halitta, ba zai yiwu ba.

Hoto: Octavio Jones/REUTERS

"Tana farowa ne daga kuruciya kuma daga nan fa ta tabbata ke nan, duk kuwa da iya kokarin da was uke yin a cewa lallai sai an canza dabi'ar, misali matsin lamba daga al'uma na ganin sai masu wannan dabi'a sun koma kamar kowa."

Binciken kimiyya dai na kan cewa dalilai masu sarkakiya ne ke musabbabin mutane su fito a matsayin masu sha'awar jinsinsu maimakon yadda aka sani bisa al'adu ta mace ta so da namji namiji kuma hankalinsa ya karkata ga ‘ya macen.

Dalilan kuwa su ne tsarin halitta da zamantakewa sai kuma tsarin halitta a kimiyyance da ya hada yadda ake samun sauyin sinadaran halitta a jiki da ake kira testesteron ke matukar tasiri a maza wajen nuna sha'awa ga danuwansu namijin kamar yadda ita ma macen sha'awarta ke zuwa ga ‘yaruwarta mace, maimakon tarayya ta gama-garin mutane.

Babban dai abin da kwararru ke nuna takaici a kan hakan, shi ne yadda kiyayyar da masu wannan dabi'a ke gani tsakanin al'uma ke shafar lafiyarsu ta kwakwalwa inda suke shiga mawuyacin hali na damuwa da kunci da kan kai su ga yunkuri na kashe kawunansu.