1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaya Kudan-zuma yake yin zuma

Abba BashirJanuary 22, 2007

Bayani akan yadda Kudan-zuma yake samar da zuma

Kudan-zuma da Fulawa
Kudan-zuma da FulawaHoto: AP

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga Malama Dije tsalha Birnin Maradi a Jamhuriyar Niger, Malamar cewa ta yi, Don Allah ina so ku sanar da ni yadda kudan zuma ke yin zuma. kuma shin,dagaskene kashin su muke sha?

Amsa: To dangane da wannan tambaya ta Malama Dije, na tuntubi Dr. Sanusu Atiku,shugaban Asibitin Dabbobi na kundila dake Jihar kano, a Tarayyar Najeriya, ga kuma amsar da ya bamu akan wannan tambaya.

Dr. Atiku: Kudan zuma wani nau’i ne na kwari da ake kira “Social insect”, wato ma’ana kwari ne da suke da tsarin zamantakewa irin na Da-adam, akwai Sarki akwai sarauniya, akwai ma’aikata, akwai sojoji, da dai sauransu.

To su kudajen zuma, Allah yasa suna samun abincinsu daga jikin furanni,a cikin furannin nan da akwai abinda suke zuwa su zuko, wani ruwa-ruwa haka, mai kamar majina, wanda a Turanci ana cewa da shi “Necter”, a Larabci ana cewa da shi Al-manna, a Hausa kuma ana kiransa Darba. To idan suka zuke shi, shine kamar abincinsu a mataki na farko.

To dama shi zuma yana da ciki kashi biyu. Kashi na farko shine abincin da ya ci a mataki na farko yake tafiya, ciki na biyu kuma shine yake karbar abincin da zai sarrafa zuma. Idan suka zuki Darbar zata shiga cikin cikin su, to akwai wasu sinadarai da ake kira enzayims, to sune zasu sarrafa wannan Darbar ta koma ta zama zuma, daya daga cikin Sinadaran ana kiransa da suna Lebules, shine idan yayi aiki akan Darbar nan sai ya canzata ta zama nau’i na suga da ake kira Lebulos,maimakon suga irin na mu da muke sha wanda ake kira Sukuros, To wannan nau’i na zuma da aka sarrafa a cikin su, shine suke kashinsa a cikin wannan Sakar tasu da suka yi, sannan kuma daga baya shine zai kasance abincinsu a mataki na biyu, shi yasa idan mutum ya je diba, wadannan sojojin na cikin su, zasu yiwo kanka suna harbin ka, domin suna kokarin su kare abincinsu ne.

Kudan Zuma na samar da zuma sama da wanda suke bukatar tarawa a sakar zuma. Sifar katangar sakar mai baki shida ta sakar zuma abu ne sananne ga kowa. Shin ka taba yin mamaki ko al’ajabi akan yadda kudan zuma yake yin sakarsa da katanga shida maimakon takwas ko biyar ?

Masana lissafi wajen neman amsar wannan tambaya sun bada cikakkiyar amsa mai ban sha’awa : Gaba shida a zane tafi dacewa wajen cikar fadin wurin da aka bayar.

Gaba shida na bukatar karancin yaukin da zata bukata wurin gina gidan zuman a yayin da zata taskace zuma mai yawa. Saboda haka ne kudan zuma ke amfani da wannan sifa a saukake. Hanyar da suke amfani da ita wurin gina gidan zuma akwai bada mamaki : kudajen zuma suna fara gina shuri ne a biyun –ukun wurare daban – daban sannan su saka ta a jikin biyun-ukun dogwayen shinge. Koda dai suna farawa ne ta wurare daban-daban, kudajen, a adadi mai yawan gaske, suke haduwa don kera wadannan gabobi shida sannan su sakata kuma su hada ta wuri guda da haduwa a tsakiya. Suzo su hade wadannan gabobin da ba zaka taba ganin alamun rabuwarsu ba.

Ta fuskar wannan kasaitaccen aiki ne, zamu tabbatar da wanzuwar iko madaukaki wanda ya tsara wadannan halittu da aikata haka.