1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Ya'yan Bazoum na son duniya ta sa baki a sake shi

Abdoulaye Mamane Amadou
November 26, 2025

Shekaru bayan hambarar da gwamnatinsa, ya'yan Mohamed Bazoum sun bukaci duniya ta sa baki a sako shi daga inda sojoji ke tsare da shi.

Tsohon shugaban Nijar Mohamed Bazoum
Tsohon shugaban Nijar Mohamed Bazoum Hoto: Stevens Tomas/ABACA/IMAGO

'Ya'yan hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, sun sake kira ga duniya ta taimaka domin ganin an sako iyayensu da ake tsare su, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2023.

Sojojin Nijar na amfani da Bazoum a matsayin garkuwa-Lauyoyi

A wani sakon da aka wallafa a mujallar Jeune Afrique, yaran tsohon shugaban sun ce hukumomin mulkin soja, sun ki su gurfanar da mahaifinsu a gaban kuliya, bisa abin da suka kira "rashin wata kwakwarar hujja kan tuhume-tuhumen da suke yi mishi," tare da bayyana cewa mahaifiyarsu ta ki barin wurin da ake tsare da mijinta kamar yadda sojoji suka ce tayi idan tana bukata, shekara guda bayan yi masa juyin mulki.

Nijar: Ko sakin Bazoum zai saukaka al'amura?

Hoto: Sophie Garcia/AP Photo/picture alliance

Guda daga cikin 'yan'yan shugaban, ta ce fiye da shekara daya, suna yin magana da iyayensu ta waya sau daya ne kawai a duk bayan makonni biyu, lamarin da suka ce shi kadai ke ba su kwarin gwiwa.

Mohamed Bazoum, da aka zaba a 2021, yana tsare tare da matarsa Hadiza a wani bangare na fadar shugaban kasa da ke birnin Niamey, tun bayan kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Rashin armashin sakin fursunonin siyasa a Nijar

Kana sojiojin da suka kifar da gwamnatinsa na zarginsa da laifin cin amanar kasa, laifin da ka iya kai shi ga hukuncin kisa a cewar masanan dokoki. Sai dai kuma lauyoyin Bazoum, sun sha bayyana irin mawuyacin halin da suka ce yake ciki tun bayan da aka tsare shi.