1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauya dubarun yaki don tabbatar da tsaro a Najeriya

August 2, 2019

A Najeriya an yaye wasu hafsan sojojin kasar bayan sun samu cikakken horon aikin soja a kokarin kara inganta tsaro da ke tabarbarewa a Najeriya, a daidai lokacin da ake ta rufa-rufa ga mutuwar wasu sojojin a fagen yaki.

Nigeria Militärpolizei in Gwagwalada
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Wasu rahotannin da wata kafar yada labarai mai zaman kanta daga wajen Najeriya sun bayyana akalla sojojin kasar dubu daya ne aka turbude a cikin sirri da nufin kin fitowa fili a bayyana iya hasarar da rundunar sojan Najeriya ta ke fuskanta a yaki da 'yan ta'adda, lamarin da ya kara haifar da zafafar mahawara tsakanin masu bukatar da a gudanar da binciken lamarin da na bangaren sojoji.

Wanan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kaddamar da bukin yaye wasu manyan hafsoshin sojan kasar 127 da suka karbi horo daga wata makarantar horon soja ta tarayyar Najeriya, inda a cikin jawabinsa Muhamadu Buhari ya tabbatar da cewa ana samun ci gaba ta fannin tsaro, tare da nuna godiya ga jami'an tsaron kasar bisa abinda ya kira jan kokarin da suke don tabbatar da tsaro a Najeriya.

Hukumomin Najeriya sun tabbatar da shigo da sauye-sauyen yaki da aiyukan ta'addanci a kasar shekaru 10 bayan ci gaba da fafatawa da kungiyar Boko Haram. A share daya daliban makarantar da aka yaye sun tabbatar da yin wani bincike na hadin gwiwa tare da cibiyar tsaro da zaman lafiya ta kasar Habasha don duba hanyoyin kyautata tsaro a nahiyar Afirka.

Masu sharhi kan a'amurran tsaro na ganin cewa da akwai bukatar saka adalci daga manyan hafsoshin yakin zuwa ga kananan da ke fagen daga ta hanyar tabbatar masu da kayan aiki irin na zamani da kuma hanyoyin inganta rayuwarsu ta yau da kullum muddin ana bukatar kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya a cikin gagawa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani