Za a tsagaita wuta a yakin Yemen
November 19, 2018Talla
Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da manzon musammun na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths zai kai ziyara kasar, domin shirya tattaunawa ta neman sulhu tsakanin bangarorin da ke yakin. Manzon na Majalisar Dinkin Duniya ya ce gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya da kuma 'yan tawayen na Houthi wadanda ke samun goyan bayan Iran, sun nuna bukatar yin tattaunawar. Mutane kusan 10,000 ne suka mutu a yakin na Yemen da ake gwabzawa tun a shekara ta 2015 yayin da wasu dubbai suka arce daga kasar.