1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen: Fada ya sake barkewa a Hudeida

Mahmud Yaya Azare GAT
November 20, 2018

Jim kadan bayan ayyana tsagaita wuta a Yemen, fada ya sake barkewa a birnin Hudeida, tsakanin 'yan tawayen Huthi da ke ikiririn ci gaba da kame garin, da dakarun kawancen Saudiyyar da ke ci gaba da yi masa lugudan wuta.

Yemen - al-Hudaida. Soldat
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Almamari

Yanzu haka dai ana ci gaba da dauki ba dadi tsakanin bangarorin biyu, wadanda suka yi ta zargin juna da keta yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a cimmata don fara tattaunawa.Kakakin rundunar kawancen na Saudiyya,Turki Al-Maliki ya ce, za su ci gaba da dakile duk wani yunkurin yin kafar ungulu ga yarjejeniyar tsagaita wutar:


“Hare harenmu za su ci gaba a birnin Hudeida, don dakile duk wani yunkurin sake baza makamai ko kokarin kame sabin wurare da 'yan Huthi ke yi a birnin na Hudeidah.”


 To sai dai a nata bangare, kungiyar ta 'yan Huthi, a ta bakin kakakinta Hameed Aaseem, ta ce, kawancen na Saudiyya na kokarin fakewa da batun tsagaita wutar ne, don cimma nasarori a fagen dagar da ya kasa cimma, duk kuwa da lugudan wuta na makwanni biyun da ya yi tayi wa birnin:

Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Mohammed


 “Mu al,ummar Yemen muna nan kan bakanmu na yaki da sojojin mamayar da ke son tursasa mana mika wuya ga azzalumai makiya, wadanda ke neman bautar da mu. Duk da cewa hakan bai nufin muna adawa da duk wata sahihiyar tattaunawar da za ta kawo karshen harin da ake kawo mana, da tabbatar da zaman lafiya.”

 

Kamar dai yadda Muhammad Shamsan, wani da ke sa ido kan yakin na Yemen ke cewa, fadan na baya-bayan nan yunkuri ne da bangarorin biyun suke na samun kakkarfar madogara a yayin tattaunawar zaman lafiyar da ake shirin yi a kasar Sweden:


“A duk lokacin da aka fara batun tattaunawar zaman lafiya, za ka ji irin wadannan hare-haren sun barke. Kowane bangare na son nuna wa duniya cewa shi ba kanwar lasa ba ne a filin daga, don cin moriyar hakan a teburun tattaunawa.”

Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Gambrell

 

Yunkurin tsagaita buda wutar dai na zuwa ne karkashin kokarin Majalisar Dinkin Duniya na farfado da tattaunawar sulhun da aka kasa yin nasara a tsawon shekaru uku da aka kwashe ana yaki a kasar, wanda ya kai ga halaka sama da mutane dubu 10, ya kuma jefa kasar cikin matsananciyar yunwa da cututtuka.