Yemen: Goyon baya ga 'yan Houthis
August 20, 2016 A watan Yulin da ya gabata ne dai 'yan tawayen na Houthis da ke zaman Musulmi mabiya Shi'a da kuma Saleh tsohon shugaban kasar da guguwar juyin-juya halin kasashen Larabawa ta yi awon gaba da gwamnatinsa, suka sanar da samar da wata majalisar gudanarwa ta hadaka. Da yake jawabi a yayin wannan zanga-zanga, shugaban mayakan na Houthis Saleh al-Samad ya ce ba da jimawa ba majalisar za ta sanar da kafa gwamnati a kasar. A nasa bangaren tsohon gwamnan birnin Aden da gwamnatin Abed Rabbo Mansur Hadi da kasashen duniya suka amince da ita ke da fadar mulki a yanzu haka, Abdulazizi Bin Habtoor ya yi karin haske kan dalilin fitowarsu wannan zanga-zanga yana mai cewa:
"Al'umma sun fito domin su nuna goyon baya ga babbar majalisa ta dimokaradiyya, mu nuna musu goyon baya a siyasance mu kuma nuna goyon bayanmu ga fafutukar da suke yi."
Masu zanga-zangar dai sun yi ta rera wakokin nuna kin amincewa da ruwan bama-baman da rundunar taron dangi da Saudiya ke jagoranta ke yi a kan al'ummar kasar mafi akasarinsu fararen hula, a kokarin rundunar na abin da ta kira kare halastacciyar gwamnatin kasar ta shugaba Abed Rabbo Mansur Hadi.