1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen: Kokarin wanzar da zaman lafiya

Ahmed Salisu
November 22, 2018

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Yemen Martin Griffiths ya yi wata ganawa da madugun 'yan tawayen Yemen kwana guda kafin ziyarar da zai kai birnin Hodeida inda ake cigaba da rikici.

Yemen Krieg Soldaten
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Mohammed

Tattaunawar ta Mr. Griffits da madugun 'yan tawayen Abdulmalik Al-Huthi ta mayar da hankali ne kan fidda matakai na wanzar da zaman lafiya a kasar wadda ta shafe tsawon lokaci cikin tashin hankali.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce tuni wasu daga cikin 'yan tawayen suka nuna sha'awarsu ta ganin an kawo karshen zub da jinin da ake yi a kasar wanda ya yi sanadin rasuwar dubban mutane yayin da wasu miliyoyi ke fusakntar barazana ta cutuka da ja'ibar yunwa.