1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yemen na fuskantar barazanar yunwa

Ramatu Garba Baba
March 2, 2021

Mutum sama da miliyan 16 za su fuskanci tsananin yunwa a sakamakon karancin kudin da ake bukata don tallafawa aiyukan jin kai a kasar da ke fama da rikici.

Jemen Protest UN Bürgerinitiative
Hoto: picture alliance/Yahya Arhab/E

Bayan gazawa a samar da tallafin kudi don kulawa da wadanda rikicin kasar Yemen ya daidaita, masu aikin agaji sun saduda tare da zurawa sarautar Allah ido a yayin da Yemen ke gab da fadawa cikin wani tsanani da ake ganin ka iya zama mafi muni a tarihi. An dai dauki dogon lokaci ana neman tallafi daga kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, Majalisar Dinkin Duniya ta iya samun dala biliyan daya da dari bakwai daga cikin dala kusan biliyan hudu da ta ke bukata don kulawa da 'yan gudun hijirar Yemen.

A wani taro da Majalisar ta gudanar a ranar Litinin da ta gabata, ta ce mutum sama da miliyan goma sha shida a Yemen ne za su fuskanci matsananciyar yunwa saboda rashin abinci.Tashin hankalin da aka kwashi fiye da shekaru takwas ana yi, ya kassara fannin lafiya da tattalin arzikin kasar tare da tilasta wa wasu sama da miliyan hudu tserewa gidajensu, annobar corona da sauran cuttutuka kamar kwalera da tamowa sun yi sanadiyar rayukan dubbai inji majalisar.