Sabon fata a Yemen bayan shekaru 10
February 10, 2021Guguwar juyin-juya halin kasashen Larabawan dai, ta yi awon gaba da gwamnatin shugaban kasar Yemen na wancan lokacin Ali Abdullah Saleh. Bukatar neman sauyi na irin kamun ludayin mahukuntan kasar ta Yemen na wancan lokacin karkashin jagorancin Shugaba Saleh ce, ta sanya matasa a kasar neman ganin ya sauka daga mulki domin maye gurbinsa da wanda suke ganin zai fi tafiyar da kasar kan tsarin da kowa zai yi farin ciki da shi.
Karin bayani: Shekaru biyar da fara barin wuta a Yemen
Guda daga cikin batutuwan da suka sanya matasa a Sanaa yanke shawarar neman shugaban ya sauka daga mulki shi ne, irin yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu a gwamnatinsa. Hakar matasan na Yeman dai ta cimma ruwa, kasancewar guguwar ta yi awon gaba da gwamnatin kasar har ma ta shiga sauran kasashe irinsu Masar, inda nan ma ta jawo samun sauyi na shugabanci.
Karin Bayani:Mahawara kan makomar kasar Yemen
Sai dai kuma lamarin ya bar baya da kura a wasu kasashen ciki har da Yemen din, domin kuwa ta shiga yakin basasar da ya yi sanadiyyar rasuwar mutanen da suka haura dubu 100 yayin da sama da mutum miliyan 20 ke fuskantar kalubale na tsaro da masifar yunwa kamar yadda Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nunar.
Wani abu kuma da rikicin na Yemen ya haifar bayan kadawar guguwar neman sauyin shi ne, takun saka da ya kara kamari tsakanin kasashen duniya musamman ma Iran da Saudiyya wanda da yawa ke kallon suna amfani da kasar wajen gwada 'yar kwanji tsakaninsu kasancewar ko wane bangare ya zabi wanda yake goyawa baya tare da bayar da kudi da makamai da ma taimako na soja.
Karin bayani: Hadaddiyar Daular Larabawa ta fice daga Yemen
To sai dai duk da irin matsalolin da kasar ta samu kanta a ciki bayan tabarbarewar lamura wanda suka kara kamari sakamakon bullar cututtuka kamar amai da gudawa da kuma annobar nan ta coronavirus a baya-bayan nan, wasu 'yan kasar da ma masharhanta na ganin ko ba komai an cimma nasara ta samun sauyin shugabanci. Guguwar neman sauyin dai ta taimaka wajen yin awon gaba da shugabannin kasashe da dama a yankin Gabas ta Tsakiya da suka shafe shekaru a kan gadon mulki, koda yake a hannu guda wasu na nuna shakku kan cimma nasarar.
Masana kamar dan fafutukar nan na Yemen wato Farea al-Muslimi na shan tambaya daga wadanda ke da tababa kan samun nasarar game da yadda suke kallon lamarin: "Ana yawan tambaya ta ko ina nadamar abin da ya faru, ko ina nadama kan shiga cikin wadanda suka assasa juyin-juya halin da aka yi. Zan so a ce in amsa musu da e, don hakan zai kawar da duk wani abu da ke kaina, sannan in samu bacci kyakkyawa. Abin da na sani shi ne, mun shiga cikin wadanda suka kafa tarihi ko kuma wadanda suka zama tarihi."
Karin Bayani: Sharhi kan rikicin siyasar kasar Yemen
Yanzu haka dai Amirka na fadi-tashi wajen ganin rayuwa ta daidai ta a kasar ta Yemen, kuma mataki na farko da ta fara dauka shi ne na ganin an kawo karshen yakin da kasar ke fama da shi. Tuni ma gwamnatin Shugaba Joe Biden ta sanar da dakatar da tallafawa Saudiyya musamman ma ta fuskar sayar mata da makamai a yakin da ake a Yemen din, sai dai wasu kwararru na ganin kamar ba da gaske Amirkan ta ke ba.