Yemen ta shiga mawuyacin hali
May 30, 2017Talla
Manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadi game da yaduwar cutar amai da gudawa da rashin abinci tsakanin milyoyin mutane a kasar Yemen, bayan kwashe shekaru biyu ana yakin basasa tsakanin bangaren gwamnati da 'yan tawayen Houthi.
Karamin-sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da jinkai Stephen Rothwell O'Bien ya ce kasar ta Yemen ta zama mafi karancin abinci a duniya, inda kusan mutane milyan bakwai suke daf da fadawa karancin abinci. Kuma ya fadi haka ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya lokaci wata muhawara. Karamin-sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da jinkai Stephen Rothwell O'Bien ya kuma ce babu fari a kasar ta Yemen amma yaki tsakanin bangarori masu rirkici da juna ya jefa kasar cikin mawuyacin hali.