1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 85 sun mutu a yayin turmutsitsi a Yemen

April 20, 2023

Akalla rayukan mutane 85 sun salwanta ciki har da mata da yara yayin da wasu mutanen fiye da 320 suka ji munanan raunika bayan aukuwar wani turmutsitsi a birnin Sanaa da ke karkashin 'yan tawayen Houthis na kasar Yemen.

Jemen | Massenpanik in Sanaa
Hoto: ANSAR ALLAH HOUTHI MEDIA OFFICE/AP/picture alliance

Turmutsitsin ya auku ne a yayin da ake rabon taimako na kudade ga marassa karfi a wata makaranta da ke wata anguwa da ake kira Bab el Yemen kamar yadda wani jami'in gidan asibitin dake karkashi 'yan tawayen da ke da iko da yankin ya tabbatar.

Har kawo yanzu dai hukumomi ba su yi bayani ba kan musabbabin tirmimutsitsin mafi muni da aka samu a tarihin kasar kana kuma ba  su fitar da alkaluman wadanda lamarin ya ritsa da su ba. 

To sai dai kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito wasu shaidun gani da ido na cewa an ji karar harbe-harben bindiga a gurin abin da ya tunzira masu karbar taimakon sun ringa shiga cikin juna.   

Wani faifan bidiyo da gidan talabijin mallakar 'yan tawayen Houtis Al Masirah TV ya wallafa ya nuna mutane na tattaka 'yan uwansu da ke zube a kasa cikin yanayi da wasunsu ba sa ma iya ko nunfashi. A wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan Yemen ta fitar ta ce an dauki nauyin wadanda suka jikkata a gidan asibi tare kuma da sanar da kama wasu 'yan kasuwa uku da su ne suka shirya rabon taimakon da kuma wani babban jami'in tsaro.