'Yan tawayen Yemen na fita daga Hodeida
December 29, 2018Talla
Kamfanin dillancin labaran Saba mai kusanci da 'yan tawayen na Houthi a kasar ta Yemen, ya ruwaito wani daga cikin jagororin 'yan tawayen na cewa tun da karfe 12 na daren Juma'a 28 ga wannan wata na Disamba ne, suka fara janyewar daga tashar jiragen ruwan birnin na Hodeida da ke zama babbar tashar da ake shigo da hajoji da kuma kayan agaji zuwa cikin kasar.
Yarjejeniyar da suka cimma a farkon watan nan na Disamba, ta kuma tanadi ficewar sojojin gwamnati daga yankunan birnin da suka sake karbewa daga 'yan tawayen, shekaru hudu bayan da mayakan na Houthi suka fatattake su daga cikinsa. Majalisar Dinkin Duniya dai ta aika da masu sa ido zuwa tashar ruwan ta Hodeida.