1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yevgeni Prigozhin ya bar kasar Belarus

Binta Aliyu Zurmi
July 6, 2023

Shugaban sojin hayan Wagner na Rasha Yevgeni Prigozhin da ya yi yunkurin tawaye ga Shugaba Vladmir Putin ya bar kasar Belarus, a cewar mahukuntan Minsk.

Yevgeny Prigozhin
Hoto: AP/picture alliance

Shugaban kasar Belarus Alexandar Lucashenko ya bayyana cewar shugaban kamfanin sojojin Wagner na Rasha Yevgeny Prigozhin ya bar kasar sa, bai baiyyana takamaimai inda shugaban Wagner ya ke ba amma ya ce ko dai yana St Petersburg ko kuma yana kan hanyar shi ta zuwa Moscow.

A baya a kokarin dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin shugaban sojin haya na Wagner da Shugaba Putin, Lukashenko ya tabbatar da isar sa birnin Minsk. An cimma yarjejeniyar kawo karshen barakar da ta kunno kai kuma an yi watsi da tuhumar da ake yi wa shugaban na Wagner.

Yunkurin yi wa Putin tawaye na zama wani babban koma baya  a daidai lokacin da suke ci gaba da luguden wuta a Ukraine.


A daya hannun kuwa, fadar mulki Rasha ta Kremlin ta chacchaki Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine a game da ziyarar da ya kai kasar Bulgaria da ke zama guda daga cikin mambobin kungiyar tsaro ta NATO.

Mai magana da yawun Kremlin, Dimitry Peskov, ya ce Ukraine na yin iya yinta na ganin ta saka wasu kasashe a fadan da ke tsakaninsu, kamar yadda take neman shafa wa Bulgaria kashin kaji. Ya kara da cewar tuni kasashe da dama a fakaice ko ma kai tsaye suka shiga wannan yakin.