Yiwuwar daukar matakin soji kan Siriya
August 28, 2013Bakin kasashen biyu ya zo daya da cewa bai wai saboda zargin amfani da makamai masu guba a kan farar hula ne za a hambarad da shugaba Assad ba. Kakakin shugaban Amirka, Jay Carney ya ce yana da muhimmaci a yi la'akari da take dokokin kasa da kasa da suka haramta yin amfani da makamai masu guba. Ita dai Amirka tana nazarin kai hare-hare akan gwamnatin Siriya.Shi kuma dai firaministan Birtaniya, David Cameron ya jadadda cewa za a takaita hare-haren ne akan kadarorin gwamnatin Siriya. Ya ce ba za a dauki wannan mataki don shiga rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ko kuma kara dagula rikicin Siriyan ba.
Shugaba Francois Hollande na Faransa ya ba da sanarwar ganawa da madugun 'yan adawar Siriya, Ahmad al-Assi al Jarba a ranar Alhamis a birnin Paris. Tun da farko Hollande ya yi bayanin cewa gwamnatin Siriya ce ke da alhakin harin gas da aka kai kusa da birnin Damaskus a wancan mako- harin da 'yan tawayen kasar suka ce ya halaka mutane sama dubu daya da dari uku.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu