1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yobe: Boko Haram sun kashe mutane da dama

Abdullahi Tanko Bala
September 2, 2024

Ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan wani mummunan hari da mayakan Boko Haram suka kai a kauyen Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

Nigeria Boko Haram Angriff in Gamboru
Hoto: AMINU ABUBAKAR/AFP/Getty Images

Wasu bayanai sun ce sama da mutane 50 suka riga mu gidan gaskiya inda wasu da dama kuma suka jikkata.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce mayakan sun shiga kauyen na Mafa a kan babura dauke da muggan makamai inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi suka hallaka jama'a suka kuma wawashe shagunan da kona gidaje da ababan hawa.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da harin sai dai ba ta baiyana alkuman wadanda suka mutu sanadiyyar harin ba kamar yadda Mataimakin Sufurtandan ‘Yan sanda Dungus Abdulkarim kakakin Rundunar ‘yan Sandan jihar ta Yobe ya shaida wa yan Jarida