1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda da Ruwanda sun musanta batun 'yan gudun hijira

Zulaiha Abubakar
April 3, 2018

Kasashen sun musanta amincewar su a kan batun karbar 'yan gudun  hijirar da ke zaune a kasar Isra'ila wadanda suka fito daga Afirka a wata sanarwar hadin gwuiwa da suka rabawa manema labarai.

Washington Israle Min isterpräsident Netanjahu bei Pk mit Trump
Hoto: picture-alliance/newscom/P. Benic

Tun da farko Firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana kin amincewarsa da shirin Majalisar Dinkin Duniya na kara tsugunar da 'yan gudun hijirar da suka fito daga Afirka a kasashen yammacin duniya a wannan Talatar, yayin da yake ganawa da wa su fusatattun jama'a mazauna kudancin birnin Tel Aviv.  

 

A halin yanzu dai Netanyahu na fuskantar Allah wadai daga kungiyoyi daban-daban ciki kuwa har da jam'iyyarsa ta Likud mai mulki a kasar.