1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda: Doka mai tsauri a kan 'yan luwadi

May 30, 2023

Matakin gwamnatin kasar Yuganda na tabbatar da dokar hukunta masu neman jinsi a kasar na fuskantar suka da turjiya daga Majalisar Dinkin Duniya da ma wasu manyan kasashen duniya.

Yoweri Musevini to sign anti-LGBT law
Hoto: Themba Hadebe/AP/picture alliance

Matakin gwamnatin kasar Yuganda na tabbatar da dokar hukunta masu neman jinsi a kasar na fuskantar suka da turjiya daga Majalisar Dinkin Duniya da ma wasu manyan kasashen duniya. Dokar kamar yadda hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD ta bayyana, za ta bude wani babi ne na take hakkin masu neman jinsi da ma sauran mutane a Yugandar.

Dokar da ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ko ma kisa kan duk wanda aka samu da laifin aikata Luwadi ko Madigo

Hoto: Abubaker Lubowa/REUTERS

A baya dama gwamnatin Yuganda ta haramta mu'amalar jinsi guda ta kowacce fuska a kasar sai dai Shugaba Yoweri Yuseweni ya shawo kan majalisar kasar don samun amincewarta, in da daga bisani ya rattaba hannu kan dokar a hukumance, dokar da ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ko ma kisa kan duk wanda aka samu da laifin aikata Luwadi ko Madigo a kasar da ke yankin Kahon Afirka, shakka babu dokar ba ta yi wa masu mu'amalar jinsi daya a kasar dadi ba,  DeLovie Kwagala daya daga cikin 'yan kungiyar ta LGBTQ+ ta ce, ina ake son su sa kansu? ''Ina ake son mu koma, ba a son ganin mu a kasar, ga shi ba a ba mu damar yin aiki ko karatu ba, hatta magani, ana kama mu tare da tsaremu ba tare da mun aikata wani laifi ba, ta ya za a mayar da mu 'yan gudun hijira a kasarmu ta asali?

Kasashen yammacin duniya sun yi barazana ga Yuganda saboda daukar matakin

Hoto: picture-alliance/dpa

Mu'amalar jinsi daya haramun ne a kasashen Afirka akalla talatin sai dai Yuganda, ce kasa ta farko da ta soma daukar matakin tsaurara hukuncin da ta tanadar ta hanyar karfafa dokar da ta tanadi daurin shekaru ashirin ga duk wanda aka kama na yada koda manufar baya ga hukuncin kisa ga gawartattun masu aikata laifukan Luwadi da Madigo da kuma hukunci na dabam ga wadanda ke yada cutar HIV/AIDS ta hanyar Luwadi. Asuman Basalirwa daya daga cikin 'yan majalisar kasar da ya jagoranci matakin ganin an amince da kudirin dokar ya ce, dama majalisar ba ta da zabi face ta yi na'am sannan daga bisani ya yi shagube ga kasashen yamma da ke suka tare da barazanar janye tallafin da suke bai wa kasar....''Ina gayyatar Amirka da Kanada da Britaniya da ma daukacin kasashen Kungiyar tarayyar Turai da su gaggauta soke takardar visar Shugaba Museveni da na sauran 'yan majalisar kasar na shiga Amirka, kai a daina bai wa duk 'yan kasar Yuganda visar shiga Amirka da Kanada da sauran kasashen Turai.'' Kungiyoyi masu aikin agaji na Amirka a kasar ta Yuganda sun dai ci gaba da baiyana fargabarsu kan tasirin dokar ga tallafin kudin da suke samu wajen aiwatar da ayyukansu a kasar a yayin da masu sharhi kan harkokin yau da kullum ke cewa, sauran kasashe kamar Tanzaniya da Kenya da ke makwabtaka da Yuganda, ka iya yin koyi da Yuganda a haramta Luwadi da Madigo a kasashensu.