LafiyaAfirka
Hadari ya halaka mutane 46 a Yuganda
October 22, 2025
Talla
A wannan Laraba wani gagarumin hadarin manyan motocin safa-safa biyu da kananan motocin sun halaka mutane 46 a babbar hanyar yammacin kasar Yuganda.
'Yan sanda sun ce akwai wasu mutanen da suka samu raunika sakamakon wannan mummunan hadarin da ya ritsa da motoci.
Akwai matafiya da dama da ba su san halin da suke ciki ba, bayan wannan hadari, wadanda ake ci gaba da kula da lafiyarsu.
Kasar Yuganda da ke gabashin Afirka tana fama da matsalolin hadari kan hanyoyin kasar inda a shekarar da ta gabata ta 2024, fiye da mutane 5,100 suka mutu a kasar sakamakon hadura na motoci.