1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda na shan suka kan dokar luwadi

Ramatu Garba Baba MAB
May 30, 2023

Amirka na sahun gaba a sukar gwamnatin Yuganda kan sabuwar dokar kasar da ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ko kisa kan masu laifin luwadi da madigo. Yuganda na shan suka kan sabuwar dokar.

Masu mu'amalar jinsi daya a Yuganda na sukar dokar hukunt luwadi da madigoHoto: Themba Hadebe/AP/picture alliance

Shugaba Joe Biden na Amirka na daga cikin shugabanin kasashen Yamma da suka soki matakin da gwamnatin kasar Yuganda ta dauka na haramta mu'amalar jinsi daya a kasar, ya na mai cewa, hakan ya tauye hakkin dan adam. Wannan tsokacin shugaban ya kuma hada da barazanar katse tallafin da Amirka ke bai wa kasar tare da dakatar da zuba jari a kasar da ke yankin kahon Afirka.

A ranar Litinin (29.05.2023) ne, shugaban kasar ta Yuganda Yoweri Museveni ya rattaba hannu kan dokar da ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ko ma kisa kan duk wanda aka samu da laifin yin luwadi ko madigo a kasar, dokar da tuni ta janyo martani na suka daga kasashen Yamma.