1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Yuganda: Noman itatuwan marmari

March 8, 2017

Eric Kaduru da matarsa Rebbeca wadanda suke tafiyar da sana´ar itatuwar kayan marmari, sun gano noma a tsayin wata hanyar karfafawa 'ya'ya´mata da suka bar makaranta gwiwa na dogaro da kai.

Uganda Bio-Landbau
Hoto: DW

Bayan yin wasu bincike, Eric Kaduru ya gano cewar kusan babu harkokin noma a kasarsa, amma akwai wadatar kasa. Shekaru hudu a baya, ya tabbatar da cewa hakan zai iya zama hanyar kasuwanci mai riba mai tsoka kana da alfanu ga al´ummar yankin karkara akasar Uganda, saboda haka ya kirkiro da wani kamfani mai suna Kad Afirka da ke da burin tallafa wa 'ya'ya mata.

"Muna kirkirar canji a zamantakewa.muna sa mutane suna ganin, harkan ilimin noma; kan ba wai aikin bane amma yanda albarkar noma take. Mun soma daukarsa a matsayinn harkar kasuwanci. Don haka baya ga koyar da yara mata fasahar rayuwa, harkokin kasuwanci, muna kuma nuna musu yadda zasu tafiyar da harkokin kudi, suna kallon hanyoyi daban daban da zasu iya ganin ilimin noma wata hanya ce mai sauki da za´a bi wajan shiga. Inhar kasan kana da wani dan fili da za ka iya kasuwanci da shi."

Yawanci manoman kasar Uganda suna shuka tsirai ne don su ciyar da kansu da iyalensu, aikine da mata suka fi yin shi. Yanda babbar aiki kamar wannan ke tafiya, ba´a bukatan hanyoyi masu tsawo. Yan matan da Cibiyar kula da walwalar jama´a ta horar duk wadanda suka bar makaranta ne. Suna samun dama ta biyu wanda ba kasafai ba ake samu ba, don su yi dogaro da kansu kana su ringa biya wa kansu bukatu. A cikin su akwai Kengisa Ennete, Kafin ta shiga Kad Afrika tana samun dala uku ne duk wata, amma yanzu tana samun har dala hamsin.

Alawa daga itatuwan marmariHoto: AP

 

"Ina adana kudina a cikin wata kungiyar adashe. Ni da sauran yan´matan da ke karkashin Kad Afrika muke wannan tafiyar da kungiyar, idan na amshi nawa kason kudin sai na soma nawa shirin. zan yi noma ko in shiga wani harkar kasuwanci dabam ko nayi siya da siyarwa don intaimaki kaina".

Da zarar an horar, matan sukan samu sha´awar shuka 'ya'yan itatuwa, a kasar da Kaduru ke basu haya a coci. A matsayin sa na dan kasuwa mai adalci, yakan siya amfanin gona su a farashin kudin kasuwa kana sai ya rarrabar, asiyar dasu.

Bayan shekaru hudu, KadAfrika din ce da kanta ke samar da fiye da kashi hamsin cikin 100 na kudaden shigar ta. Sauran aikin sha´anin kudi na samuwa ne daga cikin gida. Akalla yan mata 1700 ne suka yi shirin a cewar Kaduru, amma ya ce  har yanzu dole ya shawo kan jama´a kan kyama da akeyi wa noma, wanda ake gani a matsayin sana´a ce ta talaka.

"Amma idan ka kalla a zahirin halin da ake ciki, kowa na bukatar kai abinci bakinsa. Don haka canja tunanin mutanen yankunan karkara su dunga ganin noma a matsayin sana´a ba wai aiki ba, shi ne babbar matsalar mu."

Wannan shi ne babban kalubalen da al'umman ke fuskanta a kasar Yuganda. Yammacin Uganda na da a kalla hekta miliyan 19 na kasar noma, sai dai kashi daya cikin 100 ne na kayan itatuwa da kayan lambu ake nomawa a yankin.