1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yuganda ta bindige 'yan ta'addar da suka dana mata bam

November 19, 2021

Rundunar 'yan sandan Yuganda ta bindige mutane biyar da take zargi da hannu a tagwayen hare-haren bam da aka kai wa babban birnin kasar Kampala a ranar Talatar da ta gabata.

Großbritannien London 2020 | Yoweri Museveni, Präsident Uganda
Hoto: Henry Nicholls/REUTERS

Mai magana da yawun 'yan sanda Fred Enanga ya shaida wa taron 'yan jarida cewa bincikensu ya nuna cewa 'yan kungiyar ta'addanci ta ADF ne suka kai harin, sun kuma samu galaba a kansu a artabun da suka yi na ranar  Alhamis a yayin da mayakan na ADF ke kokarin komawa kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo, inda suke labewa.

 'Yan sandan na Yuganda sun ce sun kuma yi nasarar kama karin wasu 'yan ta'addar ADF guda 21 a yayin artabun na kan iyaka da suka yi. Tagwayen hare-haren na Bom din da ADF ta yi wa Yuganda a ranar Talata tuni suka yi ajalin mutum hudu yayin da ake ci gaba da duba lafiyar wasu fararen hula da suka ji rauni a asibiti.