1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude makarantun boko a Yuganda

Abdul-raheem Hassan MAB
January 10, 2022

Gwamnatin Yuganda ta bude makarantun boko a kasar bayan da ta rufe a watan maris na 2020 kusan shekaru biyu saboda annobar corona.

Uganda I Schule I Bildung I Coronavirus
Hoto: Badru Katumba/AFP/Getty Images

Rufewar makarantun bokon Yganda kusan shekaru biyu ita ce rufe makarantu mafi dadewa a duniya da ta shafi tabarbarewar ilimin dalibai a cewar hukumar UNICEF.

Jami'an kasar Yuganda na fargabar kashi uku bisa hudu na yaran da suka koma makarantun na cikin hatsarin kamuwa da coronar, lamarin da ka iya kawo cikas ga makomar masu tasowa. Sai dai Munir Safieldin, shi ne wakilin UNICEF a Yuganda "UNICEF ba za ta ba da shawarar rufe makarantu na tsawon lokaci haka ba. Mun yi imanin cewa ko da yaushe akwai hadarin bude makarantu saboda kuna da dalibai miliyan 15 a Yuganda, amma kamar yadda na fada, akwai matakai daban-daban na hana yaduwar cututtuka ta hanyar ilimi."