1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masunta 33 sun shiga kurkuku a Yuganda

Abdul-raheem Hassan
July 28, 2018

Wadan da aka yakewa hukuncin zaman gidan yari 'yan asalin kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ne da masu kura da kamun kifi suka kama suna su a tabkunan kudancin Yuganda ba bisa ka'ida ba.

Ugandans Kazinga Kanal Edward-See
Hoto: picture-alliance/Anka Agency International

Wata kotu a kasar Uganda ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu zuwa uku ga masuntan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango 33, kotun dai ta ce ta sami mutanen da saba ka'idojin yin su tabkunan mafi tasiri a kudancin kasar.

Wani jami'in kula da ayyukan su a Yuganda ya ce wannan hukuncin ba ya nufin cin fuskan ga makociyar kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sai don nuna bukatar bin dokokin kamun kifi.

An dau lokaci ana samun tsamin dangantaka kan rikicin kamun kifi tsakanin mazauna yankunan da ke kan iyakar kasashen biyu, abinda ke haifar da zaman doya da manja tsakanin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Yuganda.