SiyasaAfirka
Kungiyoyi masu zaman kansu na cikin tasku
November 18, 2024Talla
Lauyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Yuganda sun bayyana cewa an samu raguwar rigistan kungiyoyi masu zaman kansu sakamakon tsauraran matakan da gwamnati ta dauka kan kungiyoyin wadda take cewa sun zama 'yan aiken kungiyoyin kasashen duniya. A shekara ta 2021 gwamnatin ta rufe kungiyoyin masu zaman kansu 54 wadanda ta ce sun gaza cika sharudan da aka gindaya. Sannan tun bayan annobar cutar corona virus gwamnati ta karfafa matakan dakile kungiyoyi masu zaman kansu.
Karin Baynai: An yanke wa 'yan adawa 16 hukunci kan yaudara a Yuganda
Shugaba Yoweri Museveni na kasar ta Yuganda ya shafe shekaru 38 yana rike da madafun ikon kasar da ke yankin gabashin Afirka, kuma yana kara daukan matakan dakile 'yancin fadin albarkacin baki.