Zaben Yuganda da batun tattalin arziki
January 13, 2021Gabanin zaben na Yuganda, hasashe ya nuna karancin samun bunkasar tattalin arzikin kasar a wannan shekara, sakamakon rashin tabbas a bangaren siyasa gami da matsalar annnobar da ake ciki. Yayin da yakin neman zabe ya bunkasa harkar kasuwanci bayan kullen da aka fuskanta, ga Hussein Masha wanda yake wallafa hotunan 'yan takara na ganin wannan karon akwai tsaiko idan aka kwatanta da zabukan da suka gabata: "A shekara ta 2016, abu ne mai kyau, mun samu kudi lokacin zabe. Yanzu yanayin da muke ciki abin takaici ne, ba za mu kwatanta da lokutan baya ba."
Karin Bayani:Bobi Wine ya zame wa Yuganda ala-kakai
Hakan dai ya faru ne sakamakon yanayin tattalin arzikin kasar ta Yuganda. Tun farko ana tunanin samun bunkasar tattalin arzikin da kaso shida cikin 100. Amma annobar cutar coronavirus ta rage kimanin rabi. Yanzu akwai zaman zullumi gabanin zaben, sannan tattalin arzikin sannu a hankali yake farfadowa musamman a gajeran lokaci.
William Kizito na zama masanin tattalin arziki: "Ga mai saka hannun jari a kasa, idan aka duba gaba daya ba sa son su saka kudi a kayan abinci domin ba su san nawa za a iya sayarwa ba. Idan aka duba wadanda suke da tsari game da masana'antu akwai rashin tabbas, shin za a samu tsaro ko a'a. Saboda haka a zangon farko na shekara ta 2021, ina tunanin ba za a samu ci-gaba ba."
Karin Bayani: Museveni ya yi wa 'yan takara barazana
Tashe-tashen hankula da aka samu lokacin yakin neman zabe, sun shafi fata bisa samun farfado da tattalin arzikin ta bangaren yawon bude ido da shakatawa, wanda ya samar da kudin shiga kimanin dalar Amirka milyan dubu daya da dubu 600 a shekara ta 2019. Amma duk da haka akwai bangarorin tattalin arzuiki da ake tunanin za su samu bunkasa. Ga misali gahawa da ake fitarwa daga Yuganda ta karu a zangon karshe na shekarar da ta gabata ta 2020. Akwai kuma fata kan aikin gona zai samar da kudin da ake bukata kafin kasar ta Yuganda ta fata fitar da man fetur da iskar gas.