1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin agazawa Libiya da kuɗi

August 25, 2011

Turkiyya da Italiya sun amsa kiran neman agaji da Majalisar wucin gadin 'yan tawayen Libiya ta yi

'Yan tawayen Libiya sun kwace iko da fadar Moammar Gadhafi, dake Bab al-AziziyyahHoto: dapd

Shugaban hukumar gudanarwar majalisar wucin gadin 'yan tawayen Libiya Mahmud Jibril yayi gargaɗin cewar Libiya tana fuskantar hatsarin rarrabuwar kawunan 'yan ƙasar - muddin dai ba ta samu agajin kuɗi ba.

Tuni dama firaministan ƙasar Italiya Silvio Berlusconi ya ce ƙasar sa za ta sakewa Libiya kuɗin ta da ta sanyawa takunkumi akan sa, wanda yakai Euro miliyan 350. Hakanan ƙungiyar ƙasashen dake tuntuɓa akan rikicin na Libiya , suna ta gudanar da taruka a ƙasar Turkiyya, domin nazarin irin matakan da za su ɗauka na dai daita lamura a ƙasar ta Libiya bayan kawar da Gadhafi.

Ministan kula da harkokin wajen Turkiyya Ahmet Davutoglu ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauki matakin ɗage takunkumin da ta sanyawa ƙadarorin da Libiya ta mallaka, wanda yakai na kuɗi miliyoyin Euro.

" Ya ce akwai buƙatar mu ɗauki mataki - ta hanyar kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya domin sauƙaƙa buƙatun kuɗin da majalisar wucin gadin Libiya ke fama da su, musamman baiwa majalisar damar taɓa kuɗaɗen Libiya da aka sanyawa takunkumi yana muhimmancin gaske. Kamar yadda yanda muka tattauna a tsakanin mambobin kwamitin tuntuɓa akan Libiya Turkiyya ta riƙe kuɗi dalar Amirka miliyan 200 ne, kuma tuni ta baiwa majalisar wucin gadin zunzurutun kuɗi dala miliyan 100 a watan jiya."

Kazalilka, Davutoglu ya bayyana cewar, tilas ne ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta ci gaba da gudanar da ayyukan ta - har sai lamura sun daidaita a ƙasar ta Libiya. A ranar Alhamis dake tafe ne kuma za'a gudanar da wani babban taron sake gina ƙasar Libiya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Ahmed Tijani Lawal