Yunƙurin Amirka na canjin mulki a Siriya
August 11, 2012![US Secretary of State Hillary Rodham Clinton speaks at news conference during the ministerial meeting of the Global Counterterrorism Forum in Istanbul, Turkey, Thursday, June 7, 2012. Clinton on Thursday condemned the Syrian government for new reports of "simply unconscionable" violence, accusing President Bashar Assad of intensifying a crackdown of a national uprising that has already killed thousands. (Foto:AP/dapd)](https://static.dw.com/image/16007110_800.webp)
Talla
Hillary Clinton za ta ambato batun tallafa wa 'yan tawayen na Siriya tare da shugabanin Turkiya, da kuma maganar makomar ƙasar bayan faduwar gwamnatin Bachar al -Assad. Snnan da tabo zance agajin jin ƙai ga 'yan gudun hijiran na Siriya da ke makobciyar kasar.
Kusan 'yan gudun hijira 50.000 daga ƙasar ta Siriya suka kwarara zuwa Turkiyar tun lokacin da aka fara tashin hankalin na Siriya. A halin da ake ciki kuma faɗa na ƙara yin muni a unguwar Salhudine dake a birnin Aleppo inda 'yan tawaye suke yin yaƙin sari ka noƙe, bayan da suka janye tun canda farko.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe