1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin duniya na warware rikicin Sudan

May 18, 2012

Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi Sudan ta kwashe sojojinta daga yankin Abyei mai arzikin man fetur,

In this photo released by the United Nations Mission in Sudan (UNMIS), homes are seen burning in the town of Abyei, Sudan, Monday, May 23, 2011. Armed men burned and looted the flashpoint town of Abyei on Monday, the U.N. mission said, while Southern Sudan's military said the northern army is moving to carry out a "full-scale war" in the contested region. (Foto:UNMIS, Stuart Price/AP/dapd) EDITORIAL USE ONLY, NO SALES
Yankin Abyei mai arzikin maiHoto: AP

Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nemi gwamnatin Sudan da ta tattara nata ya nata ta fice daga yankin Abyei mai arzikin man fetur, da ta ke taƙaddama akai tsakaninta na maƙobciyarta Sudan ta kudu. Mambobin 15 na wannan kwamitin sun kuma tsawaita wa'adin aikin kiyaye zaman lafiya na sojojin Habasha 3000 da ke girka a yankin na kan iyaka tsakanin Sudan da kuma sudan ta kudu.

Tun dai watan mayu 2011 ne dai ƙasar Sudan ta mamaye yankin abyei bayan da kudancin Sudan ta kai hari kan ayarin sojojin maƙobciyarta. Ita dai Sudan ta Kudu da ta samu 'yancin cin gashin kanta a watan julin bara, ta janye nata 'yan sanda dubu bakwai daga yankin tun makon da ya gabata. Dubban fararen hula ne dai suka ƙaurace wa matsugunansu a Abye tun bayan fara sa in sa tsakanin Sudan da kuma sudan ta kudu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman