Yunƙurin girka demokaraɗiya a Tunisiya
April 27, 2011Gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Tunisiya ta haramtawa manyan jami'an gwamnati da suka yi aiki ƙarƙashin hamɓararren shugaba Ben Ali tsayawa takara a zaɓukan da za su mayar da ƙasar kan turbar demokaraɗiya. Ita dai gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin mutunta bukatar 'yan ƙasar da suka aiwatar da juyin juya hali, na nesantar da duk waɗanda suka ɗasa da gwamnatin kama karya da madafun iko. Bisa ga dokar da sabbin hukumomin Tunis suka rattaɓa hannu akai dai, duk wani mahaluki da ya taɓa riƙe muƙami mai girma shekaru goman da suka gabata, ko kuma ya ɗasa da jam'iyar Ben Ali ba shi da iko tsayawa takara. Ranar 24 ga watan Juli ne dai za a gudanar da zaɓen 'yan majalisa a karon farko ƙarƙashin hukumar zaɓe mai zaman kanta.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman