1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin Isra'ila na zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Ruth KrauseMay 31, 2012

Isra'ila ta miƙa wa Palesdinu gawawwakin mutane 91 da ke hannunta, a wani mataki na farfaɗo da shirin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya

Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu shakes hands with Palestinian president Mahmoud Abbas, at his residence in Jerusalem, Israel Wednesday, Sept. 15, 2010. Clinton is in the region for Mideast peace talks. U.S. Secretary of State Hillary Rodham Clinton on Wednesday said Israeli and Palestinian leaders are "getting down to business" on core issues of renewed peace talks, but gave no sign they are any closer to resolving a looming crisis over Israeli West Bank settlements. (AP Photo/Alex Brandon, Pool)
Netanjahu da AbbasHoto: AP

Gwamnatin Isra'ila ta miƙa gawawwakin palesdinawa 91 da ta shafe shekaru ta na riƙe da su ga hukumomin yankinsu a wani mataki da ta kira na yunƙurin jin ƙai. Ofishin firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewar ya yi hakan ne da nufin mutunta sharuɗan da aka gindaya da za su kai ga samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin gabas ta tsakiya. An gudanar da addu'o'i da kuma bikin karrama gawwakin 'yan palesdinun da suka yi fafutukar ƙwato wa yankinsu 'yanci a fadar mulki ta Ramallah, kafin daga bisani a miƙasu ga hannayen iyali da sauran dangi.

Tun a ranar 14 ga wannan wata na mayu ne Netanyahu ya yi alkawarin miƙa gawawwakin 'yan palesdinu da suka rasa rayukansu tun daga lokacin mamaya ta 1967 wato 45 ke nan da suka gabata. Daga cikin waɗannan gawawwakin kuwa, har da na dangin wani sojan ƙundunbala na ƙasar Lebenon. Wannan yunƙurin ya zo ne a daidai lokacin da shugaban Jamus Joachim Gauk ya ke kammala ziyarar aiki na kwanaki huɗu a yankin gabas ta tsakiya da nufin ƙarkafa ɗankon zumunci da kuma gano hanyoyin girka zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi