1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin Jamus na samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

May 29, 2012

Shugaba Joachim Gauk na Tarayyar Jamus ya gana da takwaran sa Shimon Peres na Isra'ila, inda ya bayyana masa cewa Jamus za ta ci gaba da kare muradun bani Yahudu.

Israel's President Shimon Peres shakes hands with his German counterpart Joachim Gauck (R) before the start of a welcoming ceremony for Gauck in Jerusalem May 29, 2012. REUTERS/Ronen Zvulun (JERUSALEM - Tags: POLITICS)
Shugaba Joachim Gauck na Jamus da takwaransa na Shimon Peres na Isra'ilHoto: Reuters

Shugaba Joachim Gauk na Jamus ya fara ziyarar aiki da ke zama na farko a yankin gabas ta tsakiya tun bayan ɗarewarsa kan karagar mulkin ƙasarsa. A lokacin da ya isa Isra'ila inda ya gana da shugaban ƙasa Shimon Peres, Gauk ya jadadda aniyar Jamus na kare muradin bani yahudu da kuma ci gaba da ƙarfafa dankon zumunci tsakanin ƙasashen biyu. Hakazalika, shugaban na Jamus ya nuna mahimmacin samar da 'yantaciyyar ƙasar Palesɗinu a yankin gabas ta tsakiya. Game da batun shirin nukuliyar Iran kuwa, Joachim Gauk ya ce babbar barazana ce ga ƙasar Israila da ma dai yankin baki ɗaya.

Shugaba ya ce Jamus za ta ci gaba da amfani da hanyoyin dipolomasiya wajen ganin cewar an warware matsalolin yankin gabas ta tsakiya cikin ruwan sanyi. Joachim Gauk da kuma takwaran aikinsa na IsraIla Shimon Peres sun halarci bikin tunawa da kisan kiyashi da aka yi wa yahudawa, inda suka ajiye furanin da nufin karrama yahudawa miliyon shida da 'yan nazis suka hallaka. Ranar alhamis ne idan Allah ya kaimu shugaba Gauk na Jamus zai isa birnin Ramallah domin ganawa da shugaban palesdinawa Mahmood Abbas.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita:Usman Shehu Usman