1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin kawo ƙarshen tarzoma a Yemen

April 20, 2011

Kwamitin sulhun MƊD ya gaza cimma matsaya game da ƙoƙarin warware rikicin Yemen dake ci gaba da janyo mutuwar jama'a

Zaman taron kwamitin sulhun MƊDHoto: dapd

A karon farko kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya tafka muhawara akan rigingimun dake wanzuwa a ƙasar Yemen, inda masu zanga zuanga ke neman kawo ƙarshen mulkin shekaru 32 da shugaban ƙasar Ali Abdallah Saleh ke yi. Sai dai kuma tattaunawar ta watse ne ba tare da kwamitin ya cimma matsaya ɗaya ba domin kuwa wasu mambobin kwamitin sun nuna sha'awar tuntuɓar gwamnatocin su gabannin cimma duk wani ƙudiri.

Jamus ce dai ta buƙaci kwamitin ya gudanar da zama na musamman domin duba rikicin ƙasar ta Yemen, kana jakadan Jamus a Mjalisar Ɗinkin Duniya Peter Wittig ya shaidawa manema labarai cewar ya yi ƙira ga bin lamura sannu a hankali da kuma gudanar da tattaunawa - a siyasance a tsakanin ɗaukacin ɓangarorin dake cikin rigimar. Taron kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniyar dai ya zo ne a dai dai lokacin da jami'an tsaron ƙasar ta Yemen suka buɗe wutar da ta sanadiyyar mutuwar masu zanga - zangar nuna adawa da gwamnati har su uku a ranar Talatar nan, a ƙoƙarin da suke yi na daƙile boren nuna ƙyamar gwamnatin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala