1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin neman canji gwamnati a Angola

August 16, 2012

Gabannin zaɓɓuɓukan gama gari da za a yi a ƙarshen wannan wata a Angola jama'a na neman kifar da gwamnatin José Eduardo Dos Santos

Supporters of UNITA, the principal opposition party in Angola, scream during a party meeting in Casenga, Angola, 03 September 2008. The Angolan elections will be held 05 September 2008. EPA/JOAO RELVAS (zu dpa 0286) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/ dpa

Carbono Casiniro wani maƙakin Hip Hop ne da ke a Luanda babban birnin Angola tare da yaran wɗanda suka raira waƙe na zambo ga gwamnatin kama karya ta Dos Santos bari ma a ji kaɗan daga cikin abinda ya ke faɗa .ya ce ''Angola na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya masu arzikin ma'adinai na ƙarƙashin ƙasa, amma du da haka matasa na fama da talauci da rashin aikin yi, ga cin hanci , da karɓar rashawa da ma tursasawa da suke fuskanta daga jami'an gwamnati, ya ce abin ya kai mana karo shi ya sa muka bi sahun yan siyasa da sauran ƙungiyoyin masu yin zanga zanga a kan titi.''

Sama da shekaru 30 Shugaban ƙasar na riƙe da madafun iko

Tun a shekara ta 1975 lokacin da Angolar ta samu yancin kai jam'iyyar MPLA (mouvement pour la liberation de L'Angola ta ke jan ragamar, mulkin ƙasar a ƙarƙashin jagoranci shugaba Dos Sontos, kana zaɓen na ƙarshen wannan wata da za a yi shi ne na ukku da aka shirya a ƙasar tun daga waccan lokaci.

Shugaban Jose Eduardo dos SantosHoto: picture-alliance / dpa

A duk zaɓen da ake yi ƙasar jam'iyyar ta MPLA ita ce ke samun gaggarumar nasara misali a zaɓen da aka yi a shekara ta 2008 jam'iyyar ta wasashe kashi 80 cikin ɗari yayin da babbar abokiyar adawarta ta UNITA ke da kashi 10 kwai cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa.Abinda ya sa yan dawar birnin da ƙauye suka shiga yin gangamin siyasa kai a kai domin samun canjin mulki

Fafutukar yan adawa da ƙungiyoyin fara fula na samun canjin mulki

''Wannan a wajan wani ganganin siyasar kenan a birnin Luanda inda wani jagoran yan adawar ya ke fatikar da jama'ar cewar su kirshe domin kawo ƙarshen mulkin zalumcin wanda ke cikin hannun tsurarun mutane da ke yin watanda da arzikin ƙasar''.Ko da shi ke ma hukumomin na ɗaukar matakan tsaro domin haramta zanga zanga amma jama'ar na sanar da juna ta hanyoyin wayar salula da shafin sada zumunata irin su Facebook da Twiter da dai sauran su .Sannan ayar tambyar da al' ummar da masu fafutukar ke yi shi ne cewar sakamakon juyin juya halin da ya auku a cikin ƙasashen larabawa shugabannin irin su Hosni Mubarak na Masar , da Ben Ali na Tunisiya da Muammar Gaddafi na Libiya duk sun kau, mi zai hana shugaba Dos Sontos ɗan kama karya wanda ba a taɓa zabensa ba tafiya.Brigadeiro na ɗaya daga cikin waɗanda ke shirya gamgamin siyasar.ya ce ''ba mu barin yin gwagwarmayya, ba sai mun kai ga cimma nasara girka cikkaken tsarin mulkin dimokaradiyya a ƙasar mu''..

Jagoran yan adawa na UNITA Isaias SamakuvaHoto: picture-alliance/dpa

Ga dai abin da sabon kudin tsarin mulkii na Angola ya tanada wanda aka amince da shi a shekara ta 2010 jagoran siyasar da jam'iyyar sa ta samu rinjaye a zaɓen yan majalisun dokoki. To take yanke shi ne zai zama shugaban ƙasa ,kuma na sa ran Dos Sontos shi ne zai lashe zaɓen na ƙarshen wannan wata ;sai dai kafin lokcin Carbono Casiniro da abokan sa na ci gaba da sukar gwamnatin cikin waƙen su.

Mawallafi : Cascais Antonio(Abdourahamane Hassane)
Edita : Usman Shehu Usman

Daga ƙasa za a iya sauraran sautin wannan rahoto