Yunƙurin shawo kan rikicin kuɗi a Turai
June 22, 2012Shugabannin gwamnatoci da kuma kasashe hudu da suka fi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai na gudanar da wani taron koli a wannan a wannan juma'a a birnin Rome, domin ci gaba da lalubo hanyoyin magance rikicin kudi da ke addabar nahiyar. Firayim minista Italiya Mario Monti mai masaukin baki ya gayyaci takwaran aikinsa na spain Mariano Rajoy da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma shugaban kasar Faransa Francois Hollande, domin su tsayar da shawara game da mahimman batutuwan da taron koli na Eu zai mayar da hanakali a kai a karshen mako mai zuwa.
Cikin wata hira da ya yi da jaridar "Süddeutsche Zeitung" da ake bugawa a ƙasar Jamus, Monti na Italiya ya nuna bukatar hada karfi da karfe tsakanin manyan kasashen domin ganin bayan matsalar kudi da ta addabi Turai. Firimiya Monti ya kuma kara da cewa samar da tsarin banki na bai daya tsakanin kasashe da ke amfani da Euro zai taimaka wajen kawo karshen matsin tattalin arzikin da ke addabar wasu daga cikinsu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman