1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin tsagaita wuta a faɗan Isra'ila da Hamas

Usman ShehuNovember 19, 2012

Ƙasashen duniya na kai kawo don samun a tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa, inda kawo yanzu sama da mutane 90 suka mutu

Palestinians flee their homes after an Israeli forces strike on nearby a sports field in Gaza City, Monday, Nov. 19, 2012. The Palestinian civilian death toll mounted Monday as Israeli aircraft struck densely populated areas in the Gaza Strip in its campaign to quell militant rocket fire menacing nearly half of Israel's population. (Foto:Bernat Armangue/AP/dapd)
Hoto: AP

Shugaban kungiyar Hamas dake zaman hijira, Khaled Meshal ya shaidawa manema labarai cewar Hamas ba za ta dakatar da yakin ba. Saboda wanda ya fara tayar dashi, shine zai kawo karshensa. A birnin Alkahira ana ci gaba da tattaunawa a game da yiwuwar cimma kwarkwaryar yarjejeniyar sulhu da za ta kai ga tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Palesɗinawan na yankin Gaza. To amma a lokacin ganawa da yan jaridu, shugaban kungiyar ta Hamas yace ko da shike akwai yiwuwar cimma yarjejeniya game da hakan, amma akwai kuma yiwuwar kara tsanantar yakin tsakanin bangarorin biyu.

Sojan Isra'ila a kan iyakarsu da zirin GazaHoto: picture-alliance/dpa

A ranar Litinin ɗin nan jiragen saman yakin Israila sun ci gaba da kai hare-hare a wurare mallakar Palesdinawa a yankin, a rana ta shidda tun da aka fara wannan tashin hankali, inda rahotanni suka ce a yau din an kashe Palesdinawa 12, abinda ya kawo Palasɗinawan da aka kashe ya zuwa 90 tun daga makon jiya.

Ci gaba da hare-haren ta jiragen sama da kuma kara yawan sojojin Israila a kan iyakar kasar da Gaza, sun kara iza wutar zaton cewar Israilan tana shirin tura sojojin nata na kasa ne da za su mamaye yankin Gaza gaba dayansa. Yayin da kasashe suke ci gaba da kokarin ganin mayakan sun ajiye makamansu, shugaban Israila, Shimon Peres ya sake maimaita yanci da hakkin Israila na kare kanta.

Yace bisa manufa bamu so tashin wannan yaki ba. Ba burinmu bane mu shafe kungiyar Hamas, ba kuma burinmu bane mu canza matsayi ko hallin da ake ciki a Gaza. Bama bukatar tashin hankali, to amma bamu da wani zabi. Wannan shi kadai ne abin da ya rage mana.

Rokokin da Hamas ta cilla cikin Isra'ilaHoto: JACK GUEZ/AFP/Getty Images

Israilan tace ya zuwa yanzu, ta kai hare-hare kimain 1350 a Gaza, to amma har yanzu bata ci karfin mayakan Hamas ba tukuna, saboda suna ci gaba da harba rokoki zuwa yankunan dake kan iyaka da Israila. Majiyoyi suka ce mafi yawan rokokin sun fito ne daga Iran, samfurin Fajr-5, wadanda Israila tace Iran din musmaman take kera su saboda amfanin Hamas kanta.

Tun da farko a yau Litinin, sai da sakatare-janar na majaoisar dinkion duniya, Ban Ki Moon ya yi kira ga bangarorin biyu masu yaki, da juna su amince da matakan tsagaita bude wuta tsakaninsu. Yace ziyararsa a yankin yana yinta ne da nufin bada gudummuwa ga kokarin tsagaita bude wutar. Bayan ziyara a Masar, Ban zai zarce zuwa birnin Kudus kafin ya gudanar da shawarwari da shugaban Palesdinawa, Mahmud Abbas.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Usman Shehu Usman