Yunƙurin warware rikicin Sudan da Sudan Ta Kudu
April 13, 2012Talla
Sudan Ta Kudu ta bayyana cewar za ta janye dakarunta daga yankin Heglig mai arziƙin man fetur da yanzu haka su ke taƙaddama a kai da ƙasar Sudan.
Shugaban na Sudan Ta Kudun Salva Kiir ya ce ya ɗau wannan mataki sakamakon matsin lamba daga ƙasashen duniya sai dai ya ce zai yi hakan ne kawai in maƙociyar sa wato Ƙasar Sudan Ta daina amfani yankin na Heglig wajen kaiwa ƙasar farmaki.
Baya ga wannan ya ce za su janye dakarun ne da nufin gujewa wani sabon rikici tsakanin ƙasashen biyu.
A baya dai Shugaba Kiir ya ƙeƙasa ƙasa ya ƙi amincewa da kiraye-kirayen da aka yi ta yi na ya janye dakarun nasa abin da ya jawo ƙasashen duniya yin Allah wadai da wannan mataki.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammad Nasir Awal