Kawo karshen rikicin Yemen
May 2, 2016Ahmed ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce bangaren gwamnatin ya janye daga tattaunawar share fage da ke gudana a kasar Kuwait sakamakon abin da suka bayyana da cewa 'yan tawayen kasar sun kai wani sabon hari a birnin Amran na Yemen din, sai dai ya ce duka bangarorin biyu sun yi alkwarin bayar da hadin kai da kuma tabbatar da ganin sun shawo kan banbance-banbancen da ke tsakaninsu domin ganin an shawo kan rikicin kasar da ya lashe rayuka masu yawa, idan aka dawo zauren tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniyar ke jagoranta. Rikici dai ya barke tsakanin gwamnatin kasar ta Yemen da ke samun goyon bayan dakarun rundunar taron dangi da Saudiya ke wa jagoranci da kuma 'yan tawayen Houthi da suka kwace iko da Sanaa babban birnin kasar a watan Satumba na shekara ta 2014.