1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin ceto darajar Euro

February 4, 2011

Kasashen da ke amfani da kudin Euro na daukar matakai na shawo kan faduwar darajar kudin a kasuwannin duniya.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa suna tattaunawa da shugaban hukumar EU, Herman Van Rompuy.Hoto: dapd

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai masu fada aji suna ganawa a birnin Brussel, inda batun ceto faduwar darajar takardar euro ya kasance gaba a jadawalin taron. Duk da cewa taron na yau an tsara shi ne don tattauna batun makamashi, ya kuma duba kudurin da kasashen Jamus da Faransa suka gabatar, kan tsuke bakin aljihun gwamnatocin kasashen dake amfani da kudin euro, a wani mataki na tsamo su daga dimbin bashin da suka fada. A wani jawabin hadin gwiwa da suka yi wa manema labarai, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Farasa Nicolas Sarkozy, sun bayyan cewa za su yi aiki tare da shugaban hukumar Tarayyar Turai Herman Van Rompuy don yanke shawara nan da karshen watan gobe, ko za su cimma wata matsaya kan matakin bai daya na ceto takardar kudin euro.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala