1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An bullo da sabon tsarin farfado da Borno

November 16, 2020

Gwamnatin Jihar Borno a Najeriya ta kaddamar da shirin farfado da jihar mai fama da matsalar tsaro da hare-haren 'yan bindiga don inganta rayuwar al'umma da farfado da tattalin arziki. 

Symbolbild I Nigeria I Islamisten nehmen Geiseln
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Manufar shirin shi ne na sake gina jihar da samar da hanyoyin karfafa tattalin arzikin kasa da inganta ilimi da harkokin lafiya uwa uba inganta zamantakewa da wanzuwar zaman lafiya tsakanin al’umma, baya ga matakin shirin na mayar da daukacin ‘yan gudun hijira da ke cikin dari-darin komawa gida ke zaune a Maiduguri zuwa garuruwan su na asali, inda hakan zai sa gwamnatin ta rufe dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijirar kafin tsakiyar shekara ta 2021.

Hoto: Government House, Maiduguri, Borno State

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce "Ana son cimma wannan kudirin ne kan zuwa shekara 2030 kuma da yardar Allah za mu farfado da wannan al’umma da matsalar tsaro ta gurgunta duk da kasancewarta al'umma mai cike da zaman lafiya  dogaro da kai."  Gwamnan ya kuma kara da cewa kan nan zuwa 25 da ke tafe suna fatan ganin al'ummar Borno ta zama mai cike da tsaro da dogaro da albarkatun noma, kuma ma har ta kasance cibiyar kasuwanci a yankuna nahiyar Afirka musamman yankunan Afirka ta Yamma da ta Arewa.

Karin Bayani: Martani dangane da hari kan gwamna

Shirin idan an aiwatar da shi kamar yadda gwamnatin ke fata za a manta da dukkanin matsaloli da aka shiga a yankin haka kuma ilimi da tattalin arzkin kasa za su bunkasa jama’a su ci gaba da walwala fiye da yadda yake a baya. Masana  da dama na ganin wannan aiki ba kawai na gwamnatin jihar Borno ba ne kowa sai ya bada tasa gudumowar.

Karin Bayani: Ba wadatar kudin yakar ta'addanci

Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

a yayin da al’ummar jihar suka yi maraba da shirin amma su na ganin sai dole an magance matsalar tsaro da ake ciki idan har ana son samun nasarar da ake nema, duk da yake sauran fatan suke suga an aiwatar da shirin kamar yadda aka tsara saboda jihar ta koma kan ganiyarta na cibiyar kasuwanci ba kawai ta Najeriya har ma da sauran sassan kasashen yankin da na Tafkin Chadi.