Yunkurin hallaka Joachim Gauck
April 19, 2013Talla
Hukumomi a Kasar Jamus sun lalata wata wasika da aka aikewa shugaban Kasar da ake zargin tana dauke da abubuwa masu fashewa.
Mai magana da yawun Shugaban Jamus Joachim Gauck yace an samu wasikar ne yayin da ake gudanar da bincike kan wasikun da aka aiko masa ta Email, inda kwararrau suka lalata wasikar a wajen fadar Gwamnatin Kasar, inda yace haryanzu basu gano daga inda wasikar take ba.
Wani Jami'in 'yansanda masu binciken manyan laifufuka na Jamus ya tabbatar da cewa an lalata wata wasika da ake zargin tana dauke da abubuwa masu fashewa sai dai yace har yanzu suna gudanar da bincike don tabbatar da hakan.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Jaafar
Edita: Yahouza Sadissou Madobi