1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin hare-haren ta'addanci a Jamus

December 20, 2016

Jerin hare haren ta'addanci da aka yi yunkurin kai wa kasar Jamus cikin shekaru da suka gabata.

Deutschland Olympia Einkaufszentrum in München Hauptbahnhof Polizei
'Yan sanda cikin shirin ko ta kwanaHoto: picture-alliance/dpa/A. Gebert

Masu rajin kishin Islama basu saurara ba a hare haren ta'addanci da suke kaiwa ciki har da tarayyar Jamus. Sau da dama dai kasar ta Jamus ke fuskantar barazanar harin 'yan ta'adda.

Oktoba 2016 - Leipzig

A wannan rana an kama Jaber al Bakr dan Siriya a birnin Leipzig bayan da wasu yan uwansa yan Siriya suka sha karfinsa. Matashin dan shekaru 22 da haihuwa ya tanadi abubuwan fashewa inda ya yi yunkurin kai hari filin jirgin sama na Berlin. Kamar yadda yan sanda suka sanar Al Bakr ya rataye kansa a dakin da aka tsare shi jim kadan bayan da aka kama shi a Leipzig.

Jaber al Bakr wanda ya kai harin LeipzigHoto: Polizei Sachsen

24. Juli 2016 - Ansbach

Daf da kofar shiga wani wurin wasan kade kade da raye raye da aka gudanar a kowace shekara, wani matashin dan gudun hijira daga Siriya Mohammed D mai shekaru 27. ya tada da bam inda ya tarwatsa kan sa, mutane da dama sun jikkata. Mohammred D. ya nuna mubaya'a ga IS. Matashin wanda ke da tabin hankali bayanai sun nuna ya sami umarni a wayarsa ta Salula jim kadan kafin fashewar bam din. Kungiyar IS ta yi ikrarin kai harin.

'Yan sanda na binciken harin ta'addanciHoto: picture alliance/AP Photo/D. Karmann


18. Juli 2016 - Würzburg

A ranar 17 ga watan Yuli, wani matashi dan shekaru 17 dan gudun hijira daga Afghanistan ya kai hari da Wuka da Gatari akan fasinjoji a cikin wani jirgin kasa kusa da Würzburg. Mutane da dama sun sami raunuka, wasu cikin matsanayin halin rayuwa. 'Yan sanda sun harbe maharin wanda ya nemi ya gudu. Harin na da nasaba da jan hankali na masu rajin kishin Islama. Wani faifan bidiyo ya nuna matashin yana ikrari ta'asa. Daga baya kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai harn. Babu tabbas a game da ko matashin mai shekaru 17 yana da alaka da IS to amma masu bincike sun yi amannar cewa ya sami tsatsauran akida ne ta radin kai.

Jami'an rundunar 'yan sandan JamusHoto: picture-alliance/dpa/K. J. Hildenbrand


 Mayu 2016-Düsseldorf

A Düsseldorf ma an kama wasu mutane uku wadanda ake zargi da kasancewa yan kungiyar ta'adda ta IS a jihar North Rhine -Westphalia da Brandenburg da kuma a Baden-Württemberg. Hukumomi sun gano cewa suna shirin kai hari birnin tare da wani mutum na hudu kuma mai akidar Jihadi wanda aka kama a Faransa. Sun tsara mutane biyu za su tada bama bamai na harin kunar bakin wake yayin da ragowar biyun kuma za su yi amfani da bindigogi da nakiyoyi su kashe mutane masu yawa. 

Binciken harin ta'addanci a EssenHoto: picture-alliance/dpa/M. Kusch


26. Fabrairu - Hannover

A wannan rana wani matashin dan shekara 15 ya kai hari kan wani dan sanda a babbar tashar jirgin kasa na Hannover bayan da dan sandan yaa tsayar da shi domin bincike da yi masa tambayoyi. Dan sandan yaa sami raunuka da suka kai sai da aka yi masa aiki a asibiti. Matashin wanda aka cafke shi ya nuna aniya ta samun alaka da Siriya.

Wani dan ta'adda da aka gurfanar a kotuHoto: picture-alliance/dpa/B. Roessler


Fabrairu 2016 - Berlin

Bugu da kari a watan fabrairu na 2016 yan sanda a Berlin suka bankado wata aniyar wasu mutane hudu yan kasar Algeria ta kai harin bai daya a lokaci guda a biranen Berlin da North Rhine-Westphalia da jihar ÖLower Saxony dukkaninsu a nan Jamus. Tuni yan sandan suka tarwatsa wannan aniya.


Disamba 2012 - Bonn

Haka ma dai a babbar tashar jiragen kasa na birnin Bonn an sami wani kunshi dauke da bama bamai a cikin jaka ajiye a gefe.Ofishin babban mai bincike na tarayya yace wani yunkuri ne na wasu masu kaifin kishin Islama na kai harin ta'addanci. A shekarar 2013 an kama mutane hudu wadanda aka tuhuma da yunkurin harin da kuma aka gurfanar da su a gaban kotu a Düsseldorf a 2014.

Hoton mutumin da ya shiriya harin BonnHoto: picture alliance / dpa

Maris 2011 - Frankfurt am Main

A watan Maris na 2011 wani dan bindiga da ke da alaka da masu kishin Islama ya kai hari a filin jirgin sama na Frankfurt inda ya harbe tare da hallaka sojoji biyu na Amirka da kuma jikkata wasu. An yanke masa hukuncin daurin rai da rai. 

Harin ta'addanci a FrankfurtHoto: AP


Juli 2006 - Köln

A babbar tashar jiragen kasa da ke birnin Kolon an yi yunkurin kai harin da bai yi nasara ba, inda wasu mutane biyu suka sanya wasu akwautna makare da abubzuwan fashewa a cikin jirgin kasa daga Hamm zuwa Koblenz. An yi sa'a bama baman basu fashe ba. A watan Disambar 2008 kotu ta yanke wa maharin na Kolon hukuncin daurin rai da rai.

Wani da ake zargi da ta'addanci a KotuHoto: AP