1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin kai hare-hare na ta'azzara a Maiduguri

March 24, 2017

Kungiyoyin kare hakin mata gami da al'ummar birnin Maiduguri na bayyana damuwa kan yadda Kungiyar Boko Haram ke zafafa kai hare-haren kunar bakin wake a birnin.

Nigeria Boko Haram Aufräumarbeiten nach Selbstmordanschlag in Maiduguri
Matasa na tattara baraguzai bayan wani hari a MaiduguriHoto: picture alliance/AP Photo/J. Ola


Sama da watanni uku ke'nan kungiyar Boko Haram ke zafafa kai hare-haren kunar bakin kusan kowane mako a wuraren taron jama'a musamman masallatai ko kuma sansanonin 'yan gudun hijira a Maiduguri, inda ake samun hasarar rayuka da dukiyoyi da dama. Haka a iya cewa kusan kullum sai jami'an tsaron ko kuma matasa masu ayyukan sa kai na CJFT sun dakile hare-haren kunar bakin wake cikin dare ko da sanyin asubahi wanda yawanci aka fi amfani da mata masu kanan shekaru.

Mata na fuskantar tarin matsaloli a wannan rikici

Yachilla Bukar ta Radio Dandak Kura tare da 'yan gudun hijiraHoto: DW/T.Mösch

Kungoyin mata sun bayyana damuwa kan yadda ake amfani da mata wasu kanan shekaru wajen kai hare-haren kunar bakin wake a wannan lokaci. Hajiya Ya Gana Alkali ita ce shugabar gamayyar kungiyoyin mata ta Najeriya reshen jihar Borno ta bayyana yadda suke ji da wannan hali da ake fama da shi a Maiduguri a matsayin wani babban kalubale da ya kamata kowa ya bada nashi taimako dan ganin masu wannan akidar basu samu nasara ba.

Karuwar harin kunar baki wake a birnin Maiduguri dai ya sa al'ummar yin tambayar makasudin dawowar hare-haren bama-baman. gwamnan Jihar Borno kashim Shetima a wata tattaunawa da muka yi da shi ya bayyana cewa abin da ya ke faruwa abin bakin ciki ne kuma gwamnati na daukar matakai don magance matsalar.

Gwamnati ta dukufa wajen neman zaman lafiya

Sojojin Najeriya a bakin aiki na tsaro a MaiduguriHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Sai dai duk da irin wadan nan hare-hare da ake kaiwa harkoki na yau da kullum na ci gaba da gudana, inda mutane ke zuwa kasuwanni da wuraren ibada ba tare da zullumi ko fargabar wani abu zai same su ba. A wurare kamar Post Office da Custom da kuma bakin kasuwar Monday Market za a lura cewa mutane suna sha'anin kasuwancinsu cikin cinkuso kuma babu wasu matakai na tsaro da a zahiri za'a ce an sa don magance irin hare-haren da ake kaiwa.