1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin karfafa dangantakar Isra'ila da Afirka

Muhammad Nasiru AwalJuly 5, 2016

A cigaba da ziyarar kwanaki hudu da yake kaiwa a wasu kasashe hudu na yankin gabashin Afirka, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yada zango a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Kenia, Benjamin Netanjahu und Uhuru Kenyatta
Hoto: Reuters

Netanyahu ya ce ya kamata Isra'ila da Kenya su yi aiki tare wajen yaki da ayyukan tarzoma. A ganawar da ya yi da wasu shugabannin Afirka a ranar Litinin a Yuganda, zango farko na wannan ziyarar Firaministan na Isara'ila ya jaddada muhimmanci hada karfi da karfe don yakar masu kaifin kishin addini. Mohammad Nasiru Awal na dauke da karin bayani.

Firaministan na Isra'ila Benjamin Netanyahu da yanzu haka yake kasar Kenya zai tattauna da Shugaba Uhuru Kenyatta a kan batutuwan da suka shafi yaki da ta'addanci sai makamashi da aikin gona. A lokacin da ya isa birnin Nairobi karkashin tsauraran matakan tsaro, Netanyahu ya ce Kenya da Isra'ila na fuskantar kalubale iri daya na ta'addanci, inda ya yi nuni da harin shekarar 2013 da aka kai wasu rukunin kantuna na Westgate mallakar Isra'ila da a birnin Nairobi, inda wasu 'yan bindiga hudu suka hallaka akalla mutane 67.

Ya ce: "Ba bu wata hujja ta aikata ta'addanci da kashe rayukan wadanda ba su san hawa ba su san sauka ba. Dole ne mu yi tir da dukkan nau'o'i na ta'addanci ko da a ina ne kuwa aka aikata su, ko a Paris ko a Brussels ko a Nairobi. Dole ne m u yi aiki tare don kare makomarmu."

Netanyahu da Yoweri Museveni na YugandaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Wandera

A ranar Litinin a matakin farko na ziyararsa a kasar Yuganda Netanyahu ya kai ziyarar filin jirgin saman Entebbe inda aka kashe dan uwansa a wani lamari na garkuwa da mutane a shekarar 1976.

A shekarun baya dai huldar dangantaka tsakanin kasashen Afirka da Isra'ila ta yi tsami. Ga misali rikicin Larabawa da Isra'ila a shekaru gommai na 1960 ya gamu da martani mabambamta tsakanin kasashen Afirka da wasunsu ke gwagwarmayar neman 'yancin kai. Sai dai a jawabin sake tarbar Isra'ila a Afirka, Shugaban Yuganda Yoweri Museveni ya yi kira da warware rikici tsakanin Isra'ila da Palastinawa nan ba da jimawa ba.

Ya ce: "Hanya daya tilo ita ce bangarorinku guda biyu su amince su zauna kafa da kafa, cikin aminci da zaman lafiya tare kuma da amincewa da iyakokin juna. An bata lokaci mai yawa an kuma ga munanan tashe-tashen hankula. Amma ban ga wata hanya da ta fi ta neman zaman lafiya ba."

Ziyarar ta Netanyahu na da nufin karfafa dangantakar diplomasiyya da ma ta kasuwanci da nahiyar Afirka, kamar yadda ya yi karin bayani a wata ganawa da ya yi da shugabannin kasashen Yuganda da Habasha da Kenya da Sudan ta Kudu da Ruwanda da Tanzaniya da kuma Zambiya a birnin Kampala .

Benjamin NetanyahuHoto: Getty Images/AFP/R. Kabuubi

Ya ce: "Muna cikin wani sauyi a huldodi dangantaku tsakanin Isra'ila da Afirka, da muka fara a nan wurin. Hakan ya tabbata samakamon canje-canjen da ke aukuwa a duniya. Mun taba kasancewa cikin kyawawan huldodin ci gaba a fannoni da dama, amma a lokaci guda muna fuskantar kalubale da ke barazanar mayar da hannun agogo baya."

A ranar Laraba Netanyahu zai kai ziyara kasashen Ruwanda da Habasha.